Gwamnatin Nasarawa ta ba ’yan gudun hijira kayan agaji

Gwamnan Jihar Nasarawa Umaru Tanko Al-Makura ya bukaci al’ummar jihar musamman wadanda ke fada da juna su mayar da wukakensu cikin kube su rungumi akidar yafiya da zaman lafiya don ba gwamnati damar ci gaba da samar musu da ribar dimokuradiyya.  Gwamna Umaru Tanko Al-Makura ya yi wannan kira ne a Lafiya a lokacin da […]

Gwamnatin Nasarawa ta ba ’yan gudun hijira kayan agaji
Gwamnatin Nasarawa ta ba ’yan gudun hijira kayan agaji

Gwamnan Jihar Nasarawa Umaru Tanko Al-Makura ya bukaci al’ummar jihar musamman wadanda ke fada da juna su mayar da wukakensu cikin kube su rungumi akidar yafiya da zaman lafiya don ba gwamnati damar ci gaba da samar musu da ribar dimokuradiyya. 

Gwamna Umaru Tanko Al-Makura ya yi wannan kira ne a Lafiya a lokacin da yake raba kayan agaji ga wadanda rikice-rikicen kabilanci suka shafa don ba su damar komawa gidanjensu.
Ya ce ya zame wa gwamnatinsa dole ta tallafa wa ‘yan gudun hijirar da kayan idan aka yi la’akari da asarar da suka yi sakamakon rigirgimun don ba su damar soma sabuwar rayuwa. Ya ce gwamnatinsa tana kashe makudan kudi don tabbatar da ‘yan gudun hijirar sun koma gidajensu musamman a yanzu da ake shirye-shiryen zaben 2015 don su samu damar zaben wadanda suke so su shugabance su cikin lumana.
Gwamna Al-Makura ya ce gwamnatinsa ta kammala shirye-shiryen tura isassun jami’an tsaro da za su raka ‘yan gudun hijirar kuma su ci gaba da kare lafiyarsu da hana aukuwar tashin-tashina nan gaba.
Wadannan jami’an tsaro a cewarsa za a bude musu sansanoni a manyan garuruwa da ake samun tashin-tashina da suka hada da Assakio da Daddare da Agyaragu da Obi da Doma da Fadamar bauna da Bakin-Rijiya da Bakin Kogi da Sabon Gida da Iggah da kuma Uggah, inda za su rika sintiri a sauran kauyuka don tabbatar da zaman lafiya mai dorewa.
Sarakunan yankunan da rigirgimun suka shafa da z asu jagoranci rabon kayan sun jinjina wa Gwamna Al-Makura kan wannan karamci inda suka yi alkawarin nuna gaskiya a wajen rabon kayayyakin ga wadanda za su amfana. Sun kuma nanata kira ga al’ummominsu kan su yafe wa juna su kuma koma gidajensu don shirye-shiryen noma. Kayan tallafin sun hada da buhunan siminti da kwanon rufi da kusoshi da katifu da buhunan wake da masara da sabulan wanka da na wanki da suturu da sauransu.