Gwamnatin Nasarawa ta fara biyan diyya ga masu filayen da za a gina filin jirgin sama

Gwamnatin Jihar Nasarawa ta ce za ta kashe sama da Naira miliyan 260 wajen biyan al’ummar garin Kwandare wadanda ginin sabon babban filin jirgin sama zai shafi filayensu. Kwamishinan Filaye da Tsara Birane na Jihar Injiniya Soni Agasi ne ya bayyana haka a Lafiya lokacin da raba cekin kudi ga masu filayen. Kwamishina Agasi ya […]

Gwamnatin Nasarawa ta fara biyan diyya ga masu filayen da za a gina filin jirgin sama
Gwamnatin Nasarawa ta fara biyan diyya ga masu filayen da za a gina filin jirgin sama

Gwamnatin Jihar Nasarawa ta ce za ta kashe sama da Naira miliyan 260 wajen biyan al’ummar garin Kwandare wadanda ginin sabon babban filin jirgin sama zai shafi filayensu.
Kwamishinan Filaye da Tsara Birane na Jihar Injiniya Soni Agasi ne ya bayyana haka a Lafiya lokacin da raba cekin kudi ga masu filayen.
Kwamishina Agasi ya ce gwamnati ta dauki matakin biya diyyar ne bisa tsare-tsarenta na tabbatar ba ta ci zarafi ko amanar kowa ba a yayin gudanar da aikin. Daga nan sai ya shawarce su kan su yi amfani da kudin yadda ya kamata inda ya ce idan aka kammala ginin filin jirgin, su da ’ya’yansu da jikokinsu ne za su fi amfana da aikin.
Da yake nuna godiyansu a madadin wadanda aka raba musu cekin kudin Alhaji Musa Bawa ya bayyana gwamnatin Umaru Al-Makura da gwamnati mai adalci da kaunar talakawa inda ya ce za su yi amfani da kudin wajen samo wasu filaye daban a yankin.
Rabon cekin kudin ya samu halartar jami’an gwamnati da sarakunan gargajiya da galibinsu daga yankin Kwandare, inda a jawabansu na fatar alheri suka jinjina wa gwamnatin jihar game da biyan diyyar.