Gwamnatin Nasarawa tana cin moriyar makwabtaka da Abuja – Daraktan NAGIS
Sabon Daraktan Hukumar Kula da Harkokin Filaye na Jihar Nasarawa, (Nasarawa Geographic Information Serbice- NAGIS), Mista Sonny Agassi ya ba da tabbaci cewa hukumar za ta kara yawan kudin shigarta daga Naira biliyan 2 da take turawa asusun gwamnatin jihar a kowace shekara, zuwa Naira biliyan 3 a shekarar nan ta 2019. Daraktan ya bayyana […]
Daraktan Hukumar NAGIS, Mista Sonny Agassi
Sabon Daraktan Hukumar Kula da Harkokin Filaye na Jihar Nasarawa, (Nasarawa Geographic Information Serbice- NAGIS), Mista Sonny Agassi ya ba da tabbaci cewa hukumar za ta kara yawan kudin shigarta daga Naira biliyan 2 da take turawa asusun gwamnatin jihar a kowace shekara, zuwa Naira biliyan 3 a shekarar nan ta 2019.
Daraktan ya bayyana haka ne jim kadan bayan Majalisar Dokokin Jihar ta tabbatar da nadinsa a matsayin sabon Daraktan Hukumar NAGIS, inda ya bayyana cewa kafin a kirkiro Hukumar NAGIS da zuwan Gwamna Umaru Tanko Al-Makura, gwamnatin jihar tana samun Naira miliyan 30 ne kacal daga harkokin filayenta a kowace shekara, duk da kusacinta da Birnin Tarayya, Abuja.
Mista Agassi wanda tsohon Kwamishinan Filaye da Tsare-Tsaren Garuruwa ne, ya ce ba shakka zuwan Gwamnatin Umaru Tanko Al-Makura ne aka fara samun ingantuwar kudaden shigar kuma har yanzu a cewarsa gwamnati tana alfahari ne da filayenta da ke yankunan kananan hukumomin Keffi da Karu zuwa Abuja kasancewarsu manyan hanyoyin samun kudin shigarta.
Ya ce “Kodayake jama’a da dama sun dauka cewa gwamnatin jihar nan ta fi samun kudin shiga ne ta fannin noma, amma ina tabbatar muku cewa a yanzu filayen gwamnati da ke wadancan garuruwa da ke makwabtaka da Abuja su ne manyan hanyoyin samun kudin shiga da gwamnati ke alfahari da su a yanzu.”
“Haka kuma ina tabbatar muku cewa idan aka ci gaba da habaka wadannan filaye yadda ya dace, to babu shakka za mu iya samun fiye da Naira biliyan 3 a shekara, sannan mu kuma samu gagarumar riba da za a iya yin amfani da ita wajen gudanar da manyan ayyuka a jihar nan,” inji shi.
Ya sanar da cewa irin harkokin da ake yi da wadannan filaye na gwamnatin sun hada da gina rukunin gidajen ma’aikata ciki har da wadanda ke zama a gidajen suna tafiya aiki a Abuja da bayar da hayarsu don gina wuraran shakatawa da wasanni da gina ofishoshi da kafa kasuwanni da gina kamfanonin gwamnati da sauransu, inda ya bukaci hadin kan ’yan Majalisar Dokokin Jihar don cimma wannan kudiri.
Tun farko a jawabinsa, bayan majalisar ta amince da nadin, Shugaban Majalisar Dokokin Jihar, Alhaji Abdullahi Balarabe ya taya Mista Sonny Agassi murnar samun mukamin, inda ya bayyana cewa ba shakka nadinsa na da manufar habakawa da tabbatar da kyakkyawar amfani da filayen gwamnatin jihar musamman wadanda ke garuruwan da ke makwabtaka da Abuja.
Ya ce ba shakka a yau Hukumar NAGIS a jihar ta kai jihar sahun jihohin kasar nan da ke kan gaba wajen tabbatar da inganci da bunkasa filayen gwamnatocinsu yadda ya dace. Daga nan sai ya bukaci ya tabbatar ya yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da nasarar hukumar, inda ya tabbatar masa cewa majalisar za ta ba shi cikakken goyon baya a yayin da ya kama aiki.
A kwanakin baya ne Gwamna Umaru Tanko Al-Makura ya gabatar wa majalisar sunan Mista Sonny Agassi a matsayin sabon Daraktan Hukumar NAGIS don tantancewa.