Gwamnatin Nasarawa za ta yi biya tara ga fursunoni

Gwamnan Jihar Nasarawa Umaru Tanko Al-Makura ya bayyana niyyar gwamnatinsa na belin fursunoni, ya bayyana haka ne a jawabinsa a wajen bikin rantsar da sababbin masu ba shi shawara su 15 da manyan sakatarorin ma’aikatu hudu da aka gudanar a gidan gwamnati. Ya ce sakamakon rashin kudi da ake fuskanta a kasar nan  ya sa […]

Gwamnatin Nasarawa za ta yi biya tara ga fursunoni
Gwamnatin Nasarawa za ta yi biya tara ga fursunoni

Gwamnan Jihar Nasarawa Umaru Tanko Al-Makura ya bayyana niyyar gwamnatinsa na belin fursunoni, ya bayyana haka ne a jawabinsa a wajen bikin rantsar da sababbin masu ba shi shawara su 15 da manyan sakatarorin ma’aikatu hudu da aka gudanar a gidan gwamnati.
Ya ce sakamakon rashin kudi da ake fuskanta a kasar nan  ya sa yawancin fursunoni ba sa iya biya kudin tara  da aka yanke musu a kotuna.
 A cewarsa: “Gwamnatina ta yanke shawarar biyan tara da aka ci fursunoni sama da 80, daga mako mai zuwa don taimaka musu da kuma rage cinkuso a gidan maza. Yawancin gidajen wakafi a jihar da kasa baki daya a halin yanzu, za a ga  sama da fursunoni 1,500 a ciki.
Ya ja hankalin sababbin mashawartansa na musamman da manyan sakatarorin da ya nada su tabbatar sun gudanar da aikinsu yadda ya kamata. Don a cewarsa ya nada su ne bisa cancanta  . Ya kuma yi amfani da damar, inda ya sanar da cewa, nan gaba za a rika gudanar da taron ’yan majalisar zartarwar jihar ne, tare da sababbin masu ba shi shawara da ya nada, don su rika ba da tasu gudumawa, sabanin yadda lamarin yake a da, inda ake yi ban da su.
“Idan aka yi la’akari da irin mutanen sabuwar majalisar zartarwar gwamnatin nan, ba shakka za a samu gagarumin ci gaba a jihar nan baki daya,” inji shi.
A jawabin godiya a madadin sababbin masu bai wa Gwamnan shawara da manyan sakatarori da aka rantsar, Alhaji Ahmed Muhammed ya gode wa Gwamnan dangane da nada su a wadannan mukamai, inda ya yi alkawari ba za su ba shi kunya ba.
 Sababbin masu ba Gwamnan shawara 15 da suka hada da Mista Malo Akawu da Joseph Ogiri da Samuel Gajere da Musa Dangana da Ado Dauda Muhammed da Rayyanu Iliyasu da Muhammed Bashir da Hajara danyaro da Dabid Ayewa da Ahmed Muhammed da sauransu. Manyan sakatarorin kuma sun hada da Muhammed danladi da Aminu Abu da Ibrahim Galdima da kuma Muhammed Iliyasu.