Gwamnatin Neja ta ba kananan ‘yan kasuwa rancen Naira biliyan 1

A farkon wannan makon ne Gwamnatin Jihar Neja ta bayar da rancen Naira biliyan daya ga kananan ’yan kasuwa da masu sana’o’i su dubu 11 da 578 a karkashin wani shirin gwamnatin na tallafa wa kananan ’yan kasuwa da masu sana’o’i a jihar. Gwamnan Jihar Neja, Alhaji Abubakar Bello ya bayyana cewa gwamnati ta yi […]

Gwamnatin Neja ta ba kananan ‘yan kasuwa rancen Naira biliyan 1

A farkon wannan makon ne Gwamnatin Jihar Neja ta bayar da rancen Naira biliyan daya ga kananan ’yan kasuwa da masu sana’o’i su dubu 11 da 578 a karkashin wani shirin gwamnatin na tallafa wa kananan ’yan kasuwa da masu sana’o’i a jihar.

Gwamnan Jihar Neja, Alhaji Abubakar Bello ya bayyana cewa gwamnati ta yi haka ne domin ginawa tare da tallafa wa masu kananan ’yan kasuwa da masu sana’o’i da suke fama da karancin jari. “Wannan wata dabara ce da za ta taimaka wajen kawar da zaman kashe wando a tsakanin matasa ta hanyar samar musu da aikin yi, inda za su rika dogaro da kansu don ci gaban jihar baki daya,” inji shi.

Gwamna Bello ya yi kira ga wadanda suka samu rancen kudaden su mai da hankali wajen ganin sun yi amafani da rancen da aka ba su yadda ya kamata,  kuma su tuna cewa bashi ne aka ba su ba kyauta ba.

Shugaban kungiyar kananan ’Yan kasuwa da Masu Sana’o’i ta Jihar, Alhaji Farouk Audi ya ce sun zabo mutum dubu 11 da 578 daga dukan kananan hukumomin jihar, inda kimanin dubu 6 da 343 daga cikinsu mata ne yayin da maza suka kasance dubu 5 da 244. Ya ce wannan shiri zai taimaka wajen kawar da talauci a tsakanin al’ummar jihar tare da kawo karshen ayyukan assha don ciyar da jahar baki daya.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno