…Gwamnatin Neja ta ba wanda ya rasa iyali 8 a ambaliya tallafin Naira dubu 200

Gwamnatin Jihar Neja ta bai wa wanda ya rasa iyalai 8 a ambaliyar ruwan Suleja tallafin Naira dubu 200 da buhun shinkafa 1 da na masara 1 da na Semobita da na gishiri da bandir din kwano daya da katan daya na magi da jarkar man gyada da na manja.  Gwamnan Jihar Neja Alhaji Abubakar […]

…Gwamnatin Neja ta ba wanda ya rasa iyali 8 a ambaliya tallafin Naira dubu 200

Gwamnatin Jihar Neja ta bai wa wanda ya rasa iyalai 8 a ambaliyar ruwan Suleja tallafin Naira dubu 200 da buhun shinkafa 1 da na masara 1 da na Semobita da na gishiri da bandir din kwano daya da katan daya na magi da jarkar man gyada da na manja. 

Gwamnan Jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta ware Naira miliyan 30 domin bayar da tallafi ga wadanda ambaliyar ta shafa a ranar Juma’ar makon jiya bayan da ya kai ziyara inda lamarin ya faru, tare da kai ziyarar ta’aziyya musamman ga mutumin da ya rasa mata biyu da ’ya’ya 6 a ambaliyar, Malam Sa’adu Abubakar Asha.

Wakilinmu ya ce ya samu labarin an raba tallafin ne a shekaranjiya Laraba, inda sauran wadanda suka rasa mutum dai-dai kuma an ba su tallafin Naira dubu ashirin kowanne. Yayin da wadanda gine-ginensu ya rushe aka ba su tallafi da ya kama daga Naira dubu hudu zuwa dubu bakwai, tare da sanar da su cewa kason Gwamnatin Tarayya da Mukaddashin Shugaban kasa  Yemi Osibanjo ya ba da umarnin a ware wa jihohi 16 da ambaliyar ta shafa a sassan kasar nan na Naira biliyan 1 da miliyan 600 bai iso hannun gwamnatin jihar ba tukuna.

Sai dai Aminiya ta samu labarin cewa tallafi mafi tsoka na Naira miliyan uku da rabi an ba da shi ne ga makarantar ’ya’yan sojoji ta Command Secondary School da ke Zuma Barrack da bangaren gine-genenta ya rushe.

Gwamnatin ta Neja ta kuma gargadi wadanda ambaliyar ruwa ya shafa a kananan hukumomin Suleja da Tafa su guji sake mai da gini a gefen kogin da lamarin ya faru.

Umarnin hana mai da gine-ginen wanda Gwamna Abubakar Sani Bello ya bayar bayan ziyarar jajantawar da ya kai a ranar Juma’ar da ta gabata kamar yadda Jami’in Watsa Labarai na karamar Hukumar Suleja, Malam Jibril Bisalla ya bayyana wa Aminiya, ya ce gwamnati ta dauki matakin ne don magance aukuwar hakan a gaba. 

A ranar Lahadin makon jiya ne ambaliya ta rusa sama da gidaje dari a yankunan biyu tare da hallaka mutum 15 a unguwannin Kusfa da Checheniya da Iraki da ke Suleja da Hayin Nasarawan-Iku a yankin Tafa.