Gwamnatin Neja ta fara daukar ma’aikatan lafiya 1,000
Gwamnatin Jihar Neja ta fara daukar ma’aikata 1,000, wadanda suka hada da likitoci, ma’aikatan jinya da sauran kwararru a bangaren kiwon lafiya. Kwamishinan Lafiya a Matakin Farko amsana Jihar Neja, Dakta Ibrahim Dangana ya ce wannan kokari ne domin kara karfafa manyan asibitoci da cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko (PHCs) a fadin jihar. […]
Gwamnatin Jihar Neja ta fara daukar ma’aikata 1,000, wadanda suka hada da likitoci, ma’aikatan jinya da sauran kwararru a bangaren kiwon lafiya.
Kwamishinan Lafiya a Matakin Farko amsana Jihar Neja, Dakta Ibrahim Dangana ya ce wannan kokari ne domin kara karfafa manyan asibitoci da cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko (PHCs) a fadin jihar.
Ya bayyana haka yayin kaddamar da ranar rigakafi ta kasa, inda ya ya raba kayan bukata ga iyaye masu shayarwa, ya kuma raba babura don zagayawa yin rigakafi a fadin jihar.
Kwamishinan ya ce gwamnan jihar ya bayar da umarnin dage takunkumin da gwamnatin da ta gabata ta sanya wa ma’aikatan kiwon lafiya a jihar.
- Jami’a Ta Kafa Cibiyar Hada Magungunan Gargajiya A Gombe
- Yadda aka kashe jagoran ’yan ta’addan Katsina da yaransa
Ya kuma bayyana kokarin da gwamnatin ke yi da suka shafi inganta ma’aikatan lafiyar.
Ya ce gwamnati na duba bada damar zuwa karin karatu, da kuma inganta hanyoyin yalwata jin dadin ma’aikatan.
Za a yi hakan ne da zimmar samar da yanayi mai kyau da za su zauna a jihar, su cigaba da bada gudunmawa a fannin lafiya, a ganin yadda takwarorinsu ke tserewa zuwa kasashen ketare.