Gwamnatin Neja ta nemi hadin kan alarammomi da malaman Tsangaya
Gwamnatin Jihar Neja ta nemi hadin kan alarammomi da malaman makarantun tsangaya a jihar su bayar da hadin kan wajen tura almajiransu makarantun tsangaya na zamanin da gwamnati ta samar don samar musu da ilimin addini da na zamani. Mataimakin Gwamnan Jihar Alhaji Ahmad Muhammad Ketso ne ya bayyana haka a jawabinsa wajen kaddamar da […]
Gwamnatin Jihar Neja ta nemi hadin kan alarammomi da malaman makarantun tsangaya a jihar su bayar da hadin kan wajen tura almajiransu makarantun tsangaya na zamanin da gwamnati ta samar don samar musu da ilimin addini da na zamani.
Mataimakin Gwamnan Jihar Alhaji Ahmad Muhammad Ketso ne ya bayyana haka a jawabinsa wajen kaddamar da shirin ciyar da almajirai da marasa galihu na watan Ramadan din bana a Ma’aikatar Kula da Harkokin Addini da Yaki da Fatara.
Alhaji Ahmad Ketso ya ce almajiran da ke yawo a kan titi suna fama da wahalar ruwa da rashin abinci da sutura, inda ya ce gwamnatinsu za ta yi duk abin da ya kamata domin samar musu da ingantaccen ilimin domin su bayar da gudunmawa ga kasar nan a fannonin tattaklin arziki da ilimi.
Mataimakin Gwamnan ya yaba gudunmawar malaman addini ga harkokin ssiyasar kasar nan inda suka taimaka wajen kawo canji cikin lumana wajen zaben sababbin gwamnoni da Shugaban kasa. Ya ce wannan ya nuna cewa jama’ar Najeriya ba su kaunar duk wani abin da zai kawo cikas ga zaman lafiya.
A jawabin Babbar Sakatariya a Ma’aikatar Al’amuran Addini da Yaki da Fatara, Hajiya Salamatu Abubakar, ta ce an tsara ciyar da almajirai da marasa galihu a cibiyoyi 47 a kananan hukumomin Chanchaga da Kwantagora da Bidda da Suleja, wadanda za a sa musu ido wurin gudanar da lamarin cikin watan Ramadan.
Hajiya Salamatu Abubakar ta tunatar da wadanda aka ba alhakin kula da shirin a makarantu su ji tsoron Allah su yi amfani da kayan da aka samar yadda ya kamata, ta ce za a sa kafar wando daya da duk wanda aka kama ya saba wa tsarin ciyar da almajiran da marasa galihu, wajen samar musu da kayan da na bude baki.
Babban Limamin Minna kuma Shugaban Majalisar Limaman Masallatan Juma’a na Jihar Neja, Sheikh Ibrahim Isah Fari ya nemi wadanda za su ci moriyar shirin da sauran Musulmi su yi wa gwamnati a matakin tarayya da jihohi addu’o’in alheri wajen gudanar da mulkin jama’arsu.
Sheikh Ibrahim Isah Fari ya ce ya yi matukar farin ciki da suka samu labarin kaddamar da shirin na bana duk da matsalar rashin kudin da take ciki.