Gwamnatin Neja za ta farfado da kulob din Neja Tornadoes

Gwamnatin Jihar Neja tana yin duk abinda ya kamata domin ganin kungiyar kwallon kafa mallakarta wato Niger Tornadoes ta koma rukunin kwararru a gasar wasa ta badi idan Allah Ya kai mu a matsayin daya daga cikin matakan da take dauka na ba wasannin motsa jiki kulawar da ta kamata. Jami’in yada labarai na kungiyar […]

Gwamnatin Neja za ta farfado da kulob din Neja Tornadoes
Gwamnatin Neja za ta farfado da kulob din Neja Tornadoes

Gwamnatin Jihar Neja tana yin duk abinda ya kamata domin ganin kungiyar kwallon kafa mallakarta wato Niger Tornadoes ta koma rukunin kwararru a gasar wasa ta badi idan Allah Ya kai mu a matsayin daya daga cikin matakan da take dauka na ba wasannin motsa jiki kulawar da ta kamata.
Jami’in yada labarai na kungiyar Mista George Daniya ne ya shaidawa wakilinmu haka yayin da suka yi hira da shi ta waya inda ya tabbatar cewa gwamnatin jihar ta biya duk ‘yan wasa hakkokinsu da doka da kuma ka’idar yarjejeniyar daukarsu kwantaragin da aka saba yi duk shekara kafin su yi wa kowace kungiya wasa ko kuma sabunta kwntaragi.
Mista George Daniya ya jaddada cewa ’yan kwallon Tornadoes a yanzu suna da babban buri daya ne a wannan kasar,babban burin kuwa shi ne yin wasa a rukunin wasa na kwararru da kowane dan wasa ke muradi. Duk dan wasan da ya samu haka yana da fatan samun gayyatar yi wa kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles wasa wanda yana daya daga cikin alfaharin da cikakken ‘yan kwallo ke bugun kirji da shi.
Jami’in ya ce kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa don kula da kungiyar yana shirye-shiryen da suka kamata domin ganin kungiyar ta koma rukunin kwararru. Ya bayyana sakacin da gwamnatin baya ta yi na rashin ba ’yan kwallon kulawar da ta dace al’amarin da ta sa suka samu koma-baya.

Jadawalin Gasar Rukunin Firimiya na Ingila a Wannan Mako:
Asabar 29 ga Agusta, 2015
Newcastle United    Da         Arsenal    daya saura kwata na rana
Stoke City        Da          West Brom        Uku na rana
Manchester City    Da            Watford        Uku na rana
Liberpool        Da           West Ham United    Uku na rana
Chelsea        Da            Crystal Palace        Uku na rana
Bournemouth    Da            Leicester City        Uku na rana
Aston billa        Da            Sunderland        Uku na rana
Tottenham         Da            Eberton                      Biyar da rabi na yamma

Lahadi 30 ga Agusta, 2015
Southampton    Da    Norwich City         daya da rabi na rana
Swansea City        Da    Manchester United    Hudu na yamma