Gwamnatin Obasanjo ce ta kafa tarihin cin hanci da rashawa mafi muni a Najeriya — Fadar Shugaban Ƙasa

Obasanjo ba shi da kimar sukar gwamnati mai ci, la’akari da irin ɓarnar da ya yi a zamaninsa.

Gwamnatin Obasanjo ce ta kafa tarihin cin hanci da rashawa mafi muni a Najeriya — Fadar Shugaban Ƙasa

Fadar Gwamnatin Najeriya ta ce tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo ya daɗe da kafa tarihin zama shugaban da ya jagoranci gwamnatin da matsalar cin hanci da rashawa ta yi wa katutu mafi muni a tarihin ƙasar.

Hakan na ƙunshe ne cikin wasu jerin saƙonni na mayar da martani da mai bai wa Shugaba Bola Tinubu shawara kan sadarwa, Sunday Dare ya wallafa a shafinsa na X.

Hadimin shugaban ƙasar ya ce Obasanjo ba shi da kimar sukar gwamnati mai ci, la’akari da irin ɓarnar da ya yi a zamanin gwamnatin da ya jagoranta, ta hanyar kassara tsarin dimokaraɗiya.

A cewar Dare, a zamanin gwamnatin tsohon shugaban aka ware dala biliyan $16 don samar da wutar lantarki, maƙudan kuɗaɗen da har yanzu babu labarin inda suke, saboda kwanciyar magirbin da aka yi a kansu.

“Dukkaninmu muna sane da abin da ya faru ƙarƙashin mulkinsa [Obasanjo] da ma yadda aka yi, har zuwa yanzu, babu cikakken bayani a kan yadda aka kashe dala biliyan 16 wajen samar da megawatt ta duhu a fadin Najeriya.

“Kamata ya [Obasanjo] yi ya nemi gafarar ‘yan Najeriya saboda gazawa wajen samar da kayayyakin more rayuwa da Najeriya ke buƙata domin samun ci gaba,” a cewar Dare.

Ya ƙara da cewa, abin dariya ne Obasanjo ya riƙa faɗakarwa akan laifukan cin hanci da rashawa.

A bayan nan ne dai Obasanjo ya caccaki gwamnatin ta shugaba Tinubu yayin jawabin da ya gabatar a wani taro da ya halarta a dandalin koyar da shugabanci na Chinua Achebe na Jami’ar Yale da ke New Heaven Connecticut a ƙasar Amurka.

A jawabin nasa mai taken “gazawar shugabanci da kangin gwamnati”, Obasanjo ya bayyana halin da Najeriya ke ciki da mummuna.

Yayin taron, tsohon shugaban ya ce yanzu haka duk wasu alamu na gazawa ko rushewa daga matsayin ƙasa ya tabbata a kan Najeriya, laifin da ya ɗora a kan masu madafun ikon da ya bayyana a matsayin masu tsananin son rai, cin hanci da rashawa, rashin ɗa’a da kuma gazawa wajen shugabanci nagari.

A cewar sanarwar da hadiminsa a kan harkokin yada labarai, Kehinde Akinyemi ya fitar, Obasanjo ya yi zargin cewar a halin yanzu Najeriya na cikin wani kangin gwamnati kuma yanayin ba shi da kyau ko kaɗan.

Tsohon shugaban ƙasar ya kuma yi zargin cewa an tabbatar da matakin gazawar Najeriya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Tinubu, kuma komai ya bayyana ƙarara ga mutane masu gaskiya su gani.”

Wannan dai ba shi ne karo na farko ko na biyu da Obasanjo ke caccakar mahukuntan da suka biyo bayan gwamnatin da ya jagoranta ba, musamman ma akan fannin tattalin arziki.

DAGA LARABA: Me Ya sa Matasa Ba sa Ɗaukar Koyarwa A Matsayin Sana’a?

Cutar Anthrax ta ɓarke a Zamfara

Faston da ke yi wa ’yarsa fyaɗe tsawon shekaru ya shiga hannu

Trump ya rattaba hannu kan gomman dokokin zartarwa