Gwamnatin Ogun ta rufe kamfanoni saboda mutuwar ma’aikata
An rufe kamfanonin sakamakon haɗurran da ake samu a masana’antun da suka yi sanadin asarar rayuka.

Gwamnatin Jihar Ogun ta rufe masana’antu guda biyu, na Quantum Steel Industry da ke Ogijo, a Ƙaramar Hukumar Sagamu da kuma kamfanin Xinfeng Plastics Limited da ke kan hanyar Legas zuwa Ibadan.
An rufe kamfanonin sakamakon haɗurran da ake samu a masana’antun da suka yi sanadin asarar rayuka.
- An sako ɗaliban jami’ar da aka yi garkuwa da su a Binuwai
- An yanke wa masu fyaɗe 3 hukuncin dandanƙewa da rataya a Kaduna
An rufe kamfanin Quantum Steels saboda fashewar wani abu da ya raunata wasu ‘yan Najeriya bakwai da ma’aikata ‘yan ƙasashen waje.
Haka kuma an rufe kamfanin Xinfeng Plastics bayan da wani ma’aikacin na’ura mai suna Ishaku Monday ya rasa ransa sakamakon wutar lantarki.
Mai baiwa gwamna shawara na musamman kan Hukumar kare muhalli ta Jihar Ogun, OGEPA wanda kuma shi ne yake riƙe da matsayin shugaban kwamitin yaƙi da muhalli na jihar, Farook Akintunde ya ce gwamnati ta ɗauki matakin rufe kamfanonin ne domin gudanar da bincike kan musabbabin aukuwar lamarin cikin gaggawa da kuma samar da mafita don daƙile afkuwar lamarin nan gaba.
“A matakin gwamnati, mun ƙuduri aniyar gudanar da sahihin bincike tare da gayyato masana harkokin tsaro na waje domin gano musabbabin faruwar wannan lamari domin kare lafiyar jama’a.
“Abin da ya fi muni shi ne, duk da ziyarar da gwamnatin jihar ke kai wa waɗannan kamfanoni a kai-a kai kamar yadda sauran jihohin ke yi don wayar da kansu kan buƙatar bin ƙa’idojin tsaro, irin waɗannan al’amura sun faru a cikin gudanar da harkokin kamfanin da suke samar da su wanda ya yi sanadin asarar rayuka, don haka akwai buƙatar a rufe su,” in ji shi.
Akintunde ya ƙara da cewa kamfanonin biyu za su ci gaba da kasancewa a rufe har sai an kammala bincike tare da kafa sababbin ƙa’idojin tsaro.