Gwamnatin Osun ta bayyana Litinin mai zuwa 1 ga Muharram a matsayin ranar hutu

Gwamnatin Jihar Osun ta bayyana ranar Litinin mai zuwa 1 ga watan Muharram na shekarar 1435 BayanHijira a matsayin ranar hutu. Kwamishinan Ayyuka na Musamman na Jihar Alhaji Bashiru Ajibola ne ya bayyana haka a Osogbo a wani taron manema labarai da kungiyoyin Musulmin jihar suka shirya a ranar Litinin da ta wuce.Alhaji Bashiru Ajibola, ya […]

Gwamnatin Osun ta bayyana Litinin mai zuwa 1 ga Muharram a matsayin ranar hutu
Gwamnatin Osun ta bayyana Litinin mai zuwa 1 ga Muharram a matsayin ranar hutu

Gwamnatin Jihar Osun ta bayyana ranar Litinin mai zuwa 1 ga watan Muharram na shekarar 1435 BayanHijira a matsayin ranar hutu.
 Kwamishinan Ayyuka na Musamman na Jihar Alhaji Bashiru Ajibola ne ya bayyana haka a Osogbo a wani taron manema labarai da kungiyoyin Musulmin jihar suka shirya a ranar Litinin da ta wuce.
Alhaji Bashiru Ajibola, ya ce ranar 1 ga Muharram na shekarar Musulunci ta 1435 da ta zo daidai da ranar 4 ga Nuwamban bana gwamnatin jihar ta amince da tsayar da wannan muhimmiyar rana a matsayin ranar hutu a ko’ina cikin jihar. Ya ce, “Daga yanzu duk ranar da ta zo daidai da 1 ga watan Muharram, ta zama ranar hutu.”
Shugaban Gamayyar kungiyoyin Musulmin Jihar Osun, Sheikh Salahudeen Olayiwola, wanda ko’odinetan ayyuka Alhaji Mustapha Adeleke Olawuyi ya wakilta, ya ce, an kammala shirye-shiryen bukukuwan murnar zagayowar wannan rana da za a yi kwana bakwai ana gudanarwa a sassan jihar. “Muhimmai daga cikin abubuwan, sun hada da lacca da manyan malaman Musulunci za su gudanar a manyan makarantu domin fadakar da al’ummar Musulmi game da yadda za su gudanar da rayuwarsu kamar yadda Musulunci ya shimfida da halartar masallatan Juma’a tare da bayar da kyaututtuka don murnar zagayowar wannan rana,” inji shi.