Gwamnatin Osun ta samar da jirgin kasa kyauta ga jama’a

Gwamnatin Jihar Osun ta samar da wasu taragan jiragen kasa da suka yi jigilar ’yan asalin jihar kyauta daga Legas zuwa Osogbo domin samun saukin gudanar da bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara. Wannan ya zo ne a daidai lokacin da karancin man fetur ya haifar da karuwar kudaden shiga motocin sufuri ninkin ba ninkin a […]

Gwamnatin Osun ta samar da jirgin kasa kyauta ga jama’a

Gwamnatin Jihar Osun ta samar da wasu taragan jiragen kasa da suka yi jigilar ’yan asalin jihar kyauta daga Legas zuwa Osogbo domin samun saukin gudanar da bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara.

Wannan ya zo ne a daidai lokacin da karancin man fetur ya haifar da karuwar kudaden shiga motocin sufuri ninkin ba ninkin a sassa daban-daban na kasa.

Kwanaki biyu kafin ranar Kirsimeti ne dimbin mutane maza da mata da kananan yara da tsofaffi suka yi dafifi a tashar jiragen kasa ta Ido a Legas domin cin wannan garabasa ta shiga jirgin kasa ba tare da biyan ko kwabo ba zuwa Osogbo babban birnin Jihar Osun.

Wannan jirgin kasa da Gwamnatin Rauf Aregbesola ta samar, shi ne zai yi jigilar komawa da mutanen zuwa Legas a farkon mako na sabuwar shekarar 2018, bayan kammala bukukuwan.

Binciken Aminiya ya nuna cewa akwai mutane masu yawa wadanda ba ’yan asalin Jihar Osun ba ne da suka ci moriyar shiga cikin wannan jirgi da gwamnatin jihar ta saba tanadarwa ga jama’a a kowace shekara a lokutan bukukuwan Sallah da na Kirsimeti.

Binciken ya ci gaba da nuna cewa, kudin da fasinjoji suka saba biya a baya domin shiga motocin haya ya karu da kashi 100 bisa 100 a birane da garuruwa a sashen Kudu maso yammacin kasa. Akwai dogayen layukan abubuwan hawa a wasu gidajen sayar da man fetur da kowanne yake jiran layi ya zo kansa.

Wasu gidajen man suna sayar da lita a kan kayyadadden farashi na Naira 145 ne a yayin da wasu gidajen suke karbar na goro kafin su sayar ga mabukata.

A bangare daya kuma ’yan bumburutu ne suke cin karensu ba babbaka wajen sayar da litar man fetur daya a kan Naira 350. Mafi yawancin ’yan bumburutun matasa ne da kananan yara har da ’yan mata a cikinsu da suke gudanar cuwa-cuwar a kan manyan hanyoyi.

Tabbatattun bayanai sun nuna cewa, farashin wasu kayan abinci da na bukatun yau da gobe sun yi tashin gwauron zabo a wannan sashe na Kudu maso yammacin kasa. Hakan kuwa ya biyo bayan karancin man fetur ne da tsadarsa. Har zuwa yammacin ranar Talata da ta gabata, akwai dogayen layuka a gidajen mai a birnin Ibadan da kewaye.