Gwamnatin Oyo ba ta da niyyar hana ’yan okada zirga-zirga a jihar
Gwamnan Jihar Oyo, Sanata Abiola Ajimobi, ya ce gwamnatinsa ba ta yi wani shirin hana ’yan okada zirga-zirga a kan hanyoyin jihar ba saboda suna gudanar da halattaccen aikin da suka zabar wa kansu domin dogaro da kansu ne. A maimakon soke wannan aiki, gwamnati ta yi tanadin horar da ’yan okada da ilmantar da […]

Gwamnan Jihar Oyo, Sanata Abiola Ajimobi, ya ce gwamnatinsa ba ta yi wani shirin hana ’yan okada zirga-zirga a kan hanyoyin jihar ba saboda suna gudanar da halattaccen aikin da suka zabar wa kansu domin dogaro da kansu ne. A maimakon soke wannan aiki, gwamnati ta yi tanadin horar da ’yan okada da ilmantar da su yadda za su inganta sana’arsu.
Gwamnan ya fadi haka ne a lokacin da ya kai ziyarar jaje ga ’yan kasuwar katako ta Sango da ke Ibadan, wadanda gobara ta yi wa barna a wani sashe na kasuwar. Gwamnan, wanda ya mika gudunmawar Naira miliyan 5 ga ’yan kasuwar ya ce, irin wadannan mutane da suka kashe kudinsu wajen sayen babur domin daukar fasinja da suke samun abubuwan biyan bukatu, su ne suka zabar wa kansu yin wannan sana’ar, wacce halattacciya ce, ba a haramta ta ba, saboda haka babu wani mataki da gwamnati za ta dauka domin hana su neman halas dinsu.
Ya ce matsayin gwamnati a kan ayyukan okada a Jihar Oyo, bai wuce sanya idanu domin tabbatar da suna girmama dokoki, wajen nisantar hayaniya da tashe-tashen hankula ba. An gano cewa, ana yin amfani da wasu daga cikin masu sana’ar okada wajen yin ayyukan fashi da makami da sauran miyagun ayyuka, wanda gwamnati ba za ta amince da hakan ba, inji shi. Saboda haka daga yanzu za a fara yin rajistar dukkan ’yan okada da za a ba kowanensu katin shaida mai dauke da lambar babur dinsa. Yin hakan zai taimaka wajen rage irin barnar da ’yan fashi ke yi ta fannin amfani da babur na masu okada.
Tun da farko sai da shugaban ’yan kasuwar katako ta Sango, Mista Taiwo Faseyitan ya roki gwamnatin ta hanzarta daukar matakin sake gina kasuwar ta yadda za ta dace da zamani. Ya nuna goyon bayan ’ya’yan kungiyar a kan irin ayyukan ci gaba da gwamnati ke yi a jihar.