Gwamnatin Oyo ta daukaka matsayin hakimai zuwa sarakuna masu wukar yanka
Masarautar Ibadan mai kunshe da kananan hukumomi 11 da Sarki daya tak ta samu karin sarakunan yanka guda 21, wadanda Gwamnan Jihar Oyo Sanata Abiola Ajimobi ya mika masu takardar shaida da sandar sarauta domin tabbatar da daukaka matsayinsu daga manyan masu rike da sarautu da hakimai zuwa matsayin sarakuna. Daga yanzu wadannan sababbin sarakuna […]
Masarautar Ibadan mai kunshe da kananan hukumomi 11 da Sarki daya tak ta samu karin sarakunan yanka guda 21, wadanda Gwamnan Jihar Oyo Sanata Abiola Ajimobi ya mika masu takardar shaida da sandar sarauta domin tabbatar da daukaka matsayinsu daga manyan masu rike da sarautu da hakimai zuwa matsayin sarakuna. Daga yanzu wadannan sababbin sarakuna a masarautar ta Ibadan za su rika sanya hular sarauta kuma a rika kiran su da sunan Oba wato Sarki a maimakon tsohon sunansu na Baale wato Hakimi.
Da yake tabbatar da daukaka matsayin sababbin sarakunan a wajen wani biki da aka gudanar a babban zauren taro na Mapo da ke Ibadan a Lahadin da ta gabata, Gwamnan Ajimobi ya ce ya yi amfani da karfin iko da sashe na 28 na kundin dokar nadin sarautu na Jihar Oyo na shekara ta 2000 ya ba shi ne wajen tabbatar da daukaka matsayin sarakunan, wadanda za su ci gaba da kasancewa a karkashin kulawar Olubadan na Ibadan.
Daga yanzu, inji Gwamnan, za a rika kiran Olubadan na Ibadan da sunan Babban Mai Alfarma (Imperial Majesty) a yayin da 9 daga cikin ’yan majalisarsa masu rike da manyan sarautu a masarautar Ibadan za su rika amsa sunan Masu Alfarma (His Royal Majesty). Su kuwa Baale wato Hakimai 13 za a rika kiran su da sunan Masu Martaba (His Royal Highness) ne, wadanda aka daukaka darajar kowannensu zuwa matsayin Oba wato sarki.
Babban zauren taro na Mapo ya cika makil da mutane maza da mata da suka halarci wannan gagarumin biki da aka yi a Ibadan. Sai dai rashin halartar Olubadan na Ibadan Oba Saliu Akanmu Adetunji zuwa wajen bikin ya rage wa bikin armashi. Tun farko kafin isowar ranar bikin sai da Gwamnatin Jihar ta bayar da sanarwar cewa Olubadan na Ibadan shi ne zai zama Uban Biki, wanda Olubadan ya tsame kansa daga shiga cikin al’amarin da ya ce ba zai taba tsoma kansa ciki ba saboda akwai kara guda 2 da aka shigar a kotu da ta dakatar da gwamnati daga ci gaba da gudanar da bikin daukaka darajar wadannan sababbin sarakuna.
Olubadan na Ibadan ya yi bayanin tsame kansa daga shiga cikin al’amarin ne saboda a cewar sa, an sanya siyasa a ciki kuma maganar tana gaban kotu, inji wata takardar sanarwa da ta fito daga fadarsa kwana daya kafin a yi bikin. Ya ce bai ga dalilin da ya sa Gwamna Abiola Ajimobi yake hanzari a kan wannan al’amari da ke gaban kotu ba. Sanarwar wacce Daraktan labarai a fadar Olubadan Mista Adeola Oloko ya sanya wa hannu, ta yi bayanin tsame hannun Olubadan daga shiga cikin wannan al’amari da ya ce a kai kasuwa.
Shi ma tsohon Gwamnan Jihar Oyo, Sanata Rasheed Ladoja mai rike da sarautar Osi na Olubadan yana daga cikin ’yan majalisar Olubadan 9 da aka daukaka matsayinsu zuwa sarakuna amma bai halarci wajen bikin ba. Hakan kuwa ba zai rasa nasaba da karar da ya shigar a gaban kotu ba, inda ya ce gwamnati ta raina kotu ke nan “domin suna sane da cewa na kai karar su gaban kotu a kan batun da kotun ce kadai za ta yanke hukunci a kan kowane mataki da ya shafi wannan al’amari.”
Sai dai a cikin dogon jawabin da ya yi wa dimbin jama’a a wajen bikin, Gwamna Ajimobi ya ce gwamnatinsa ta dauki matakin daukaka matsayin masu rike da manyan sarautu da hakiman ne domin samun canji da fito da martabar masarautar Ibadan a idon duniya. Ya nuna bakin cikinsa da masu cewa ya yi haka ne domin kaskantar da darajar Olubadan da dakile al’adun gargajiya. Ya ce ba gwamnatinsa ce ta fara daukar matakin yin gyara ga kundin dokar nadin sarautu na Jihar Oyo ba. “Gwamnatocin baya ma sun dauki irin wannan mataki ta fannin kafa kwamitoci a kan wannan al’amari da muke so a yi gyara domin ya tafi da zamani,” inji shi.
Gwamnan ya shawarci Olubadan na Ibadan ya dawo daga rakiyar ’yan siyasa masu kokarin kawo koma baya ga al’amuran ci gaban masarautar Ibadan. “Kowa ya san irin wadannan mutane ’yan siyasa ne da suka sha kaye a baya, suka kasa yin hakuri, suke so su huce hushinsu a kan nuna kyama ga dukkan abubuwan ci gaba da muka bullo da su da suka kasa yin irin su a lokacin da suke mulki.”