Gwamnatin Oyo ta raba gonaki masu girman eka 250,000 kyauta

Gwamnatin Jihar Oyo ta samar da garabasar filin noma mai girman hekta dubu 200 da 50 da za ta raba wa manoma kyauta domin bunkasa harkokin gona da samar da wadataccen abinci a jihar. Yanzu haka manoma fiye da 500 ne suka fara karbar takardar form da za su cike, domin mallaka masu irin wadannan […]

Gwamnatin Oyo ta raba gonaki masu girman eka 250,000 kyauta

Gwamnatin Jihar Oyo ta samar da garabasar filin noma mai girman hekta dubu 200 da 50 da za ta raba wa manoma kyauta domin bunkasa harkokin gona da samar da wadataccen abinci a jihar. Yanzu haka manoma fiye da 500 ne suka fara karbar takardar form da za su cike, domin mallaka masu irin wadannan filayen noma.

Bayanin haka ya fito ne daga bakin Kwamishinan ayyukan gona na Jihar Oyo, Yarima Oyewumi Oyewole wanda ya ce, gwamnati ta yi wannan tanadi na bayar da filin noma mai girman hekta 250,000 kyauta ga manoma ne, domin bukatar ganin jama’a sun rungumi harkokin noma da zai janyo hankalin kasashen ketare wajen zuba jarin da zai taimaka wajen bunkasa harkokin gona da wadata jihar da amfanin gona a jihar da kasa baki daya.

Ya ce, gwamnati ba za ta soke ko kwace takardun mallakar gonakin da ta bayar ga manoman da suka yi nasarar samun irin wadannan filayen noma kyauta ba. A maimakon haka gwamnati za ta yi duk abun da take iyawa ne wajen karfafawa manoma guiwa domin a kai ga nasara.

Sai dai wani manomi da yake noman shinkafa a garin Oyo, Ustaz Tahir Zubairu ya shaida wa Aminiya cewa, labarin bayar da gonaki ga manoma kyauta da gwamnatin Jihar Oyo ta kuduri aniyar yi bai isa gare su ba. Ya ce, “a gaskiya wannan labari bai iso gare mu ba, amma tuni muka zuba kudin mu ba tare da taimakon gwamnati ba muka fara noman shinkafa a cikin manyan gonaki guda 2 a garin Oyo. Kuma mun gode wa Allah (TWT) da ya sa wa noman namu albarka ya yi kyau, wanda idan ita kanta Gwamnatin Jihar Oyo ta gani za ta yi sha’awar irin aikin da muka yi.”

A cewarsa: “Dokar hana shigowa da shinkafa daga ketare ita ce ta karfafa mana gwiwa muka rungumi noman irin shinkafa ta gida, domin goyon bayan gwamnatin tarayya a kan shirin bunkasa kasa da abinci. Kuma akwai matasa masu yawa da suka samu ayyukan yi a cikin gonakin na mu.”

Da yake amsa wata tambaya,malami kuma manomi Ustaz Tahir Zubairu ya ce: “Idan Allah ya yarda mu ma za mu ziyarci ofishin ma’aikatar gona ta Jihar Oyo domin binciken sashen da yake raba irin wadannan takardu na form domin mu samu cin wannan garabasa.” Ya jinjina wa gwamnatin jihar da ta bullo da sabon salon bayar da tallafi ga manoma kuma ya roki gwamnati tayi adalci wajen raba gonakin. Ya ce, “kamata yayi a bayar da gonakin ga ainihin mutanen da aka tabbatar da manoma ne ba ‘yan baranda masu hada baki da wasu jami’an gwamnati suna yin cuwa cuwar sayar da gonakin ga manoma ba.”