Gwamnatin Oyo ta yi damarar shawo kan rikicin manoma da makiyaya
An umarci dukkan kananan hukumomi 33 na Jihar Oyo su samar da burtalolin kiwon dabbobi ga Fulani makiyaya a yankunansu, kuma su kafa kwamitin hadin guiwa a tsakanin manoma da makiyaya a yankunansu don a rika tattaunawa akai-akai, saboda a magance fadace-fadace da ke haifar da hasarar rayuka da dukiya. Gwamna Abiola Ajimobi ne ya bayar […]

An umarci dukkan kananan hukumomi 33 na Jihar Oyo su samar da burtalolin kiwon dabbobi ga Fulani makiyaya a yankunansu, kuma su kafa kwamitin hadin guiwa a tsakanin manoma da makiyaya a yankunansu don a rika tattaunawa akai-akai, saboda a magance fadace-fadace da ke haifar da hasarar rayuka da dukiya.
Gwamna Abiola Ajimobi ne ya bayar da umarnin cikin jawabinsa da mai ba shi shawara a kan harkokin tsaro, Mista Segun Abolarinwa ya karanta a wani taron da ya kunshi wakilan rundunonin ’yan sanda da soja da kwastam da jami’an shigi-da-fici don samar da hanyar magance rikicin manoma da makiyaya.
Ya ce binciken gwamnatinsa ya nuna kowane bangare, na manoma da makiyayan, yana da kurakuran da ke haddasa sabani a tsakaninsu, shi ya sa aka shirya taron domin samar da mafita mai dorewa.
Shugaban kungiyar Miyetti Allah, reshen jihar, Alhaji Habu Bello, ya yi na’am da sabon matakin da gwamnati ta fara dauka, sannan ya bayar da shawarar sanya wakilan makiyaya a cikin kungiyar ’yan sintiri da ke yawo cikin dazuka domin magance bata-gari. “Muddin ana so al’amura su tafi daidai, ya kamata rundunonin tsaro na ’yan sintiri su kasance na hadin guiwa tsakanin wakilan manoma da Fulani makiyaya. Yin haka zai taimaka wajen kawo karshen sabani a tsakanin bangarorin biyu, ya kuma samar da adalci a hukuncin da duk za a zartar.” Inji shi.
Alhaji Habu ya bukaci gwamnati ta yi kyakkyawan bincike dangane da wasu sarakuna da garuruwansu ke kusa da kan iyakoki, wadanda suke kiran mutane daga wasu kasashe suna sayar musu da filayen noma, wanda irin wadannan mutane sukan yi mana barna, su gudu su koma kasashensu su bar na gida da jangwam.
Shi kuwa shugaban kungiyar manoma, reshen jihar, Baale Agbe, Alhaji (Cif) Yusuf Akintola, JP jinjina wa matakin da gwamnati ta dauka ya yi na samar da burtaloli ga makiyaya. Ya ce, “Hanzarta daukar wannan mataki ya nuna Gwamna Abiola Ajimobi da gaske yake yi wajen kawo karshen rikice-rikicen manoma da makiyaya, wadanda suka fara a ’yan shekaru kadan da suka wuce. Mun gode wa Allah da Ya sanya gwamnati ta fara wannan yunkuri na daukar matakin magance matsalolin.”