Gwamnatin Oyo za ta samar da burtaloli ga makiyaya

Gwamna Abiola Ajimobi na Jihar Oyo, ya amince da samar da burtaloli domin kiwon dabbobi da nufin kawo karshen rikicin manoma da makiyaya a jihar. Ya ce daga yanzu za a rika kamawa tare da hukunta makiyaya da ke dauke da bindiga a lokacin kiwo. Kuma za rika kama dukkan manomin da aka samu da […]

Gwamnatin Oyo za ta samar da burtaloli ga makiyaya

Gwamna Abiola Ajimobi na Jihar Oyo, ya amince da samar da burtaloli domin kiwon dabbobi da nufin kawo karshen rikicin manoma da makiyaya a jihar.

Ya ce daga yanzu za a rika kamawa tare da hukunta makiyaya da ke dauke da bindiga a lokacin kiwo. Kuma za rika kama dukkan manomin da aka samu da laifin kashe shanu ta hanyar zuba guba a cikin abincinsu, domin hukunta shi.

Gwamnan ya fadi haka ne a ranar Litinin da ta gabata, a wajen taron masu ruwa da tsaki a kan rikicin manoma da makiyaya a Jihar Oyo. Ya ce kisan gillar da wasu ’yan bindiga suka yi wa Fulani su 6 a kauyen Abu Gaga a karamar Hukumar Iseyin cikin makon jiya shi ne ya sa ya kira wannan taro, wanda ya samu halartar shugabannin Fulani da jama’arsu da shugabannin manoma da tasu jama’a da kwamandojin soja da ’yan sanda da sauransu.

Gwamnan ya nuna matukar farin cikinsa da irin bayanan da suka fito daga bakin bangarorin makiyaya da manoma a wajen wannan taro da suka nuna irin kyakkyawan zamantakewa da ke tsakaninsu tun farko kafin bullar irin wannan rikici da suka ce sabon abu ne da ba su san da shi a baya ba.

Da yake nuna amincewa da wasu muhimman bukatu da shugabannin manoma da makiyaya suka gabatar a wajen taron, Gwamnan ya tabbatar da matsayin gwamnatinsa a kan batun samar da burtaloli domin kiwon dabbobi a jihar. Ya nemi dukkan makiyaya su yi rajistar yawan jama’arsu da yawan dabbobinsu ga gwamnati, wanda ya ce yin haka zai yi maganin shigowar bakin Fulani da ake zargin suna tayar da zaune tsaye a jihar.

Haka kuma Gwamnan ya ce gwamnati za ta wadata rundunar hadin gwiwa ta soja da ’yan sanda da kayan aiki, da za ta rika lura da kai-kawon makiyaya a cikin dazukan da suke kiwo domin kare lafiyarsu da dabbobinsu. Ya ce daga yanzu gwamnati za ta rika daukar nauyin shirya irin wannan taro na masu ruwa da tsaki a kowane wata, domin lalubo mikakkiyar hanyar maganin rikicin manoma da makiyaya a jihar.

Mataimakin shugaban kungiyar Miyetti Allah na kasa, Alhaji Husaini Bosso da Shugaban kungiyar na Jihar Oyo, Alhaji Yakubu Bello sun yi maraba da matsayin Gwamna a kan wannan al’amari. Sun nemi sauran gwamnatocin jihohi su yi koyi da Jihar Oyo wajen samar da burtaloli ga makiyaya da tsare lafiyarsu da dabbobinsu.