Gwamnatin PDP ta wawushe Naira biliyan 100 a Neja

Gwamnan Jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello ya zargi Jam’iyyar PDP da wawushe fiye da Naira biliyan 100 daga asusun jihar ciki har da kudin adashin fansho da gwamnatin da ta gabata ta tilasta wa ma’aikatan shiga.Gwamna Abubakar Sani Bello ya bayyana ga dimbi jama’ar da suka taru a filin wasan na Kwantagora yayin da […]

Gwamnatin PDP ta wawushe Naira biliyan 100 a Neja
Gwamnatin PDP ta wawushe Naira biliyan 100 a Neja

Gwamnan Jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello ya zargi Jam’iyyar PDP da wawushe fiye da Naira biliyan 100 daga asusun jihar ciki har da kudin adashin fansho da gwamnatin da ta gabata ta tilasta wa ma’aikatan shiga.
Gwamna Abubakar Sani Bello ya bayyana ga dimbi jama’ar da suka taru a filin wasan na Kwantagora yayin da ya jagoanci yakin neman zaben ’yan takarar shugabannin kananan hukumomi na Jam’iyyar APC a jihar.
Ya shaida wa jama’ar cewa, “Wannan na daya daga cikin miyagun ayyukan da Jam’iyyar PDP ta aikata da suka jefa iyalai da dama cikin mawuyacin hali da rashin tabbas a rayuwa.”
Gwamnan ya tabbatar wa jama’ar jihar da ma’aikatan da aka cutar cewa gwamnatinsa na daukar matakan da suka dace domin magance halin tsaka-mai-wuya da aka jefa su a ciki.
Da ya juya kan zabubbukan kananan hukumomin, Gwamna Bello ya nemi jama’a su fito domin cika alkawarin da suka yi wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari na zaben Jam’iyyar APC daga sama har kasa a dukkan mazabu 274 da ke jihar.
Gwamnan ya nanata cewa, gwamnatinsa za ta samar da yanayin da zai taimaka a gudanar da mulki cikin tsarin da zai habaka walwala da tattalin arzikin yankunan karkara.Ya ce muddin suka samu nasarar aiwatar da kudirin da suka tsara wa jama’a, za su ci gaba da ganin bambanci a salon mulki a dukkan matakan mulki.
Ya ce, “Tuni muka samar da tsarin samar wa dimbin matasa ayyukan yi da suka hada da koya musu sana’o’i. Bayan haka za a koya wa wasu dabarun noman zamani a matsayin wasu hanyoyi mafiya sauki da za a rage marasa aikin yi da ke barazana ga zaman lafiyar kasa.