Gwamnatin Ribas ta amince da biyan N85,000 mafi ƙarancin albashi
An tabbatar da cewa aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashin zai fara aiki ne nan take.
Gwamnatin jihar Ribas ta amince da biyan mafi ƙarancin albashi na Naira 85,000 ga ma’aikatan jihar.
Shugaban ma’aikata na jihar, George Nwaeke, ne ya sanar da cewa Gwamnan Jihar Siminalayi Fubara ne ya amince da hakan yayin wata ganawar sirri da shugabannin ƙwadago da manyan jami’an gwamnati.
Bayan taron da aka yi Nwaeke ya tabbatar da cewa aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashin zai fara aiki nan take.
A nasu ɓangaren, Shugaban Rukunin Tattaunawar haɗin gwiwa, Chukwu Emecheta ya yaba wa Gwamna Fubara bisa biyan buƙatun ma’aikatan Jihar Ribas.
Ya nuna jin daɗinsa ga jajircewar da Gwamnan ya yi ga ma’aikata.
Shima da yake nasa jawabin, shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta NIjeriya NLC a jihar Ribas, Alex Agwanwor, ya bayyana cewa mafi ƙarancin albashin zai taimaka matuka wajen rage wahalhalun matsin tattalin arziki da ma’aikata ke fuskanta a jihar.