Gwamnatin Ribas ta ki yi min ta’aziyyar rasuwar mamata – Patience Jonathan

Uwargidan Shugaban kasa Misis Patience Jonathan ta ce har zuwa yanzu gwamnatin Jihar Ribas ba ta je yi mata ta’aziyya kan rasuwar mahaifiyarta ba. Misis Jonathan tana mayar da martani ne kan rahotannin da kafafen watsa labarai suka bayar cewa ta wulakanta Mataimakin Gwamnan Jihar, Mista Tele Iruku wanda ya je filin jirgin saman Fatakwal […]

Gwamnatin Ribas ta ki yi min ta’aziyyar rasuwar mamata – Patience Jonathan

Misis Petience JonathanUwargidan Shugaban kasa Misis Patience Jonathan ta ce har zuwa yanzu gwamnatin Jihar Ribas ba ta je yi mata ta’aziyya kan rasuwar mahaifiyarta ba. Misis Jonathan tana mayar da martani ne kan rahotannin da kafafen watsa labarai suka bayar cewa ta wulakanta Mataimakin Gwamnan Jihar, Mista Tele Iruku wanda ya je filin jirgin saman Fatakwal don taryarta a ranar Lahadin da ta gabata.
Uwargidan Shugaban kasar wadda ke magana ta bakin kakakinta Misis Ayo Adesugba, ta bayyana rahoton kafafen watsa labaran a matsayin wani shirin masu hannu a rikicin jihar domin ci gaba da shafa mata kashin kaji ta wajen nuna ta a matsayin mai girman kai.
Sanarwar ta ce, “Ya kamata a sani a yayin da kungiyoyi da dama da daidaikun mutane daga sassan kasar nan suka yi ta’aziyya ga Uwargidan Shugaban kasa da kuma Shugaban kasar kan rasuwar mahaifiyarta, babu wani jami’in gwamnatin Jihar Ribas da ya ga ya kamata ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan Shugaban kasar duk da suna da’awar Uwargidan Shugaban kasar ’yar Jihar Ribas ce. Ya kamata su koyi yadda za su rika girmama wanda ya cancanci a girmama ta yadda su ma za a girmama su.”
Uwargidan Shugaban kasar ta bukaci a daina tsoma ta a cikin rikicin siyasar jihar, inda ta zargi masu hannu a rikicin da yin amfani da kafafen watsa labarai domin aza wutar rashin zaman lafiya da kiyayya a tsakanin jama’a.
Sanarwar ta kara da cewa, “Zuwa yanzu duk wani mai hankali zai iya gano su wane ne ainihin masu son zaman lafiya da wadanda suke da’awar dimokuradiyya da sadaukar da kai ga zaman lafiya, amma suke ci gaba da zafafa harkokin siyasa.”
Ta kara da cewa, Saboda da a daina tsoma ta a takaddamar da ake yi a Jihar Ribas ce ya sa Uwargindan Shugaban kasar take kokarin ganin ziyararta zuwa jihar ta gudana cikin sirri, domin kada ta ba masu muguwar manufa damar cimma burinsu. “Kuma galibi matar Gwamnan jiha ce ke tarbar Uwargidan Shugaban kasa a duk lokacin da ta ziyarci wata jiha,” inji sanarwar.
Sai ta ce, “Wannan shi ya sa matar Gwamnan Bayelsa ta tashi daga Yenagoa ta tarbi Uwargidan Shugaban kasar. Kuma a matsayinta na ’yar Jihar Ribas, Uwargidan Shugaban kasar tana da ’yancin ziyartar jihar a duk lokacin da ta so. To, amma an tilasta mu yin tambayar: Me ya sa duk lokacin da Uwargidan Shugaban kasa ta je Jihar Ribas sai kura ta tashi?”