Gwamnatin rikon kwarya ba ta cikin tsarin mulki – Tambuwal

Shugaban Majalisar Tarayya Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya nuna rashin gamsuwa da yunkurin da ake zargin gwamnati na yi don na kafa gwamnatin rikon kwarya maimakon gudanar da zabe mai inganci a bana. Shugaban ya bayyana haka ne a ranar Lahadi a Sakkwato, lokacin kaddamar da kamfe dinsa na takarar Gwamnan Jihar Sakkwato a karkashin […]

Gwamnatin rikon kwarya ba ta cikin tsarin mulki – Tambuwal
Gwamnatin rikon kwarya ba ta cikin tsarin mulki – Tambuwal

Shugaban Majalisar Tarayya Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya nuna rashin gamsuwa da yunkurin da ake zargin gwamnati na yi don na kafa gwamnatin rikon kwarya maimakon gudanar da zabe mai inganci a bana.

Shugaban ya bayyana haka ne a ranar Lahadi a Sakkwato, lokacin kaddamar da kamfe dinsa na takarar Gwamnan Jihar Sakkwato a karkashin Jam’iyyar APC, inda ya ce dole ne masu son shigo da gwamnatin rikon kwarya su fahimci cewa hakan ba ya cikin kundin tsarin mulkin kasar nan, don haka babu wata mafita sai gudanar da zabe mai inganci.
Ya ce da yardar Allah idan aka gudanar da zabe jam’iyyarsu ce za ta lashe zaben Shugaban kasa a karkashin jagorancin Janar Muhammadu Buhari don gyara barnar da Jam’iyyar PDP ta yi.
Ya shaida w Sakkwatawa cewa zai rike amanar dukiya da rayukansu, “Amanarku da aikin da jagoranmu Alhaji Aliyu Wamakko ya yi muku zan dora daga inda ya tsaya ba tare da gajiyawa ba, bukatata a wurinku ku rika yi min addu’ar alheri kamar yadda kuke yi wa shugabanmu wanda zan gada da ikon Allah.”
Tun da farko tsohon Gwamnan Jihar Legas Alhaji Bola Tinubu ya bukaci Shugaba Jonathan ya ajiye mukaminsa, saboda bai san tarihi da girman ofishinsa ba, shi ya sa ya ce Buhari bai saya wa sojojin Najeriya koda bindiga ba lokacin da ya yi mulki a baya.
Ya ce Shugaban kasa ya manta kasar nan ta magance mayakan sa-kai har sau uku a kasashen Chadi da Saliyo da Laberiya, ban da yakar ’yan tatsine da Janar Buhari ya yi “Don haka ne muka bukaci Buhari ya dawo don kawar mana da Boko Haram tunda wannan gwamnati ta kasa,” inji Tinubu.
Ya ce kasawar Shugaba Jonathan kasawa ce ta shi kadai ba ta dukan kasa ba, musamman yadda ya kyale mutanen Arewa maso Gabas cikin kunci.
Bikin ya samu halartar gwamnonin jihohin Kwara da Edo da jiga-jigan Jam’iyyar APC na Arewa maso Yamma.
Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aliyu Wamakko da Sanata Sani Yariman Bakura da Sanata Adamu Aliero duk sun bukaci magoya bayan Jam’iyyar APC su jajirce don ganin an samu nasara a kowane mataki kuma kada su sake su sayar da kuri’arsu ga Jam’iyyar PDP.