Gwamnatin Sakkwato ta aurar da zawararwa 125

Gwamnatin Jihar Sakkwato ta cika alkawarin da ta dauka na aurar da zawarawa a ranar Juma’ar da ta gabata inda ta aurar da zawarawa da ’yan mata 125.Gwamnatin ta fara shirin bikin ne a ranar Larabar makon jiya inda aka raba kayan biki ga ma’aurata mata aka ba su turmin atamfa daidaya da farin hijabi […]

Gwamnatin Sakkwato ta aurar da zawararwa 125

Gwamnatin Jihar Sakkwato ta cika alkawarin da ta dauka na aurar da zawarawa a ranar Juma’ar da ta gabata inda ta aurar da zawarawa da ’yan mata 125.
Gwamnatin ta fara shirin bikin ne a ranar Larabar makon jiya inda aka raba kayan biki ga ma’aurata mata aka ba su turmin atamfa daidaya da farin hijabi da sadakin Naira dubu ashirin-ashirin, yayin da maza aka ba su babbar riga da ’yar ciki da wando da kwandon goro da alkawarin ba su tallafin Naira dubu ashirin- ashirin, sannan aka yi auren ranar Juma’ar.
’Yan uwa da abokan arzikin angwaye da amaren da jami’an gwamnati sun hadu a gidan gwamnatin jihar da misalin karfe hudu na yamma inda aka daura auren a cikin masallacin Gidan Gwamnatin.
Bayan kammalawa an gudanar jawabai na shawarwari ga ma’auratan, inda a jawabin Gwamna Aliyu Magatakarda Wamakko ya ja hankalin ma’auratan kan su sanya tsoron Allah a cikin halayyarsu, kuma ya bukaci mazajen su yi tsayuwar daka wurin ciyar da matansu ta hanyar neman sana’a ba yawon maula ba. “Za a kafa kwamitin da zai rika duba ma’auratan don sulhunta su idan matsala ta taso,” injin Gwamna Wamakko.
Shugaban Hada Auren Sunna, Malam Aliyu kofar Rini da Kwamishinan Jin Dadin Jama’a, Alhaji Zubairu Yari Goronyo a jawabansu sun gode wa gwamnatin jihar ne kan wannan namijin kokari da ta yi na aurar da ’yan mata da zawarawa 125 da ke jihar, kuma sun nemi ma’auratan su rike amanar junansu.
Aminiya ta gano cikin wadanda suka ci gajiyar auren zawarawa ne, Muhammad Abubakar da ke Unguwar Tudun Wada ya shaida wa wakilinmu cewa, “Shekarata 55 kuma na yanke shawara shiga wannan lamari ne domin kara mata ta biyu, kuma na dace da samun wata bazawara mai sona har ga shi yanzu ana yi mana aure. A gaskiya na gamsu da shirin da aka yi, sai dai akwai gyara a ce kowanenmu za a ba shi Naira dubu 20 a matsayin tallafi, don ni a gyara gida kawai na kashe Naira dubu 20 kuma na karbi haya. In ka duba ba mu kadai ba ne suka cika fom sauran sun gudu don sun tabbatar an karya alkawarin da aka ce kowa zai samu Naira dubu 100 da babur, amma yanzu an tsaya a Naira dubu 20.”
Shi ma Sama’ila Muhammad Akija mai shekara 55 ya ce “Wannan aure kari ne ta biyu, na samu bazawara don mata ta farko a Gumi, amma ina yin kasuwanci a fadar jihar sai na yanke shawarar shiga lamarin don na ga akwai tsabta.”
Gado dan Musulmi mai shekara 52 ya nuna farin cikinsa ga gwamnati da ta yi musu wannan taimako, kuma ya ce shi ya kara mace ta uku ne kuma tallafin da aka ba su za su ja jari don yin wata sana’a.
Auren wanda zawarawa suka fi ’yan mata yawa an gama shi lafiya tare da rabon kayan daki ga matan, inda kowace aka ba ta karamin gado mai katifa daya da kananan kujeru uku da sauran kayan gado.