Gwamnatin Sakkwato ta kashe Naira miliyan 200 kan harkar sadarwa – Kwamishina

Kwamishinan Watsa Labarai na jihar Sakkwato Alhaji Abdulkadir Jeli Abubakar ya ce gwamnatin jihar ta kashe sama da Naira miliyan 200 wajen inganta kafafen watsa labaranta a cikin shekara daya da ta yi a karagar mulki.Kwamishina Abdulkadir Jeli Abubakar ya bayyana haka ne a ranar Asabar da ta gabata a dakin taro na kungiyar ’Yan […]

Gwamnatin Sakkwato ta kashe Naira miliyan 200 kan harkar sadarwa – Kwamishina
Gwamnatin Sakkwato ta kashe Naira miliyan 200 kan harkar sadarwa – Kwamishina

Kwamishinan Watsa Labarai na jihar Sakkwato Alhaji Abdulkadir Jeli Abubakar ya ce gwamnatin jihar ta kashe sama da Naira miliyan 200 wajen inganta kafafen watsa labaranta a cikin shekara daya da ta yi a karagar mulki.
Kwamishina Abdulkadir Jeli Abubakar ya bayyana haka ne a ranar Asabar da ta gabata a dakin taro na kungiyar ’Yan Jarida Ta kasa reshen Jihar da ke garin Sakkwato. “A shekara daya na wannan tafiya da ake kira ci gaban canji da zai kammala sauran ayyukkan da muka gada daga tsohuwar gwamnati da yin wasu sababbi mun samu nasarori da dama inda muka kashe sama da Naira miliyan 200 kan harkar sadarwa don inganta yanayin aikinmu da zai sa tashoshin watsa labaranmu su koma na zamani da za su iya gogayya da takwarorinsu na duniya,” inji Kwamsihina Jeli Abubakar.
Ya ce a bisa umarnin Hukumar Kula da Gidajen Rediyo da Talabijin ta kasa (NBC) na kafafen watsa labarai su zamanantar da kafafen watsa labaransu, ya sa gwamnatin ta mayar da kafafen watsa labaranta na zamani tare da jingine tsohuwar hanya, kan wannan tsari gidan rediyon Rima da gidan talabijin na jiha da tashar kade-kade ta FM za a saya masu kayan aiki na sama da Naira miliyan 143, bayan gyaraWA da inganta hukumar watsa labarai ta jihar da aka kammala kuma ya ci Naira miliyan 30.
Kwamishinan ya ce gidan jarida na jihar da ya rika daukar kayansa zuwa neman dab’i a wajen jihar gwamnati ta ware sama da Naira miliyan shida domin sayo kayan aikin dab’i ya ci gaba da buga jaridun a Sakkwato. “Gidan watsa labarai na Rima da aka yi watsi da shi da ke Tudun Wada wannan gwamnati ta yanke shawarar sanya kayan zama na jin dadi a ofisoshinsa na Naira miliyan 10 da dubu 40 da 872,” inji Kwamishinan.
Ya ce a fili yake irin hobbasar da ma’aikatar ta yi cikin shekara daya na gwamnatin, baya ga dimbin shirye-shirye da take da su don ciyar da jihar gaba, inda ya ce kofarsu a bude take ga duk wanda yake neman karin bayani daga gwamnati kafin ya buga labarinsa domin kauce wa sanya mutane cikin rudani da kuskure.