Gwamnatin Sakkwato ta nemi malaman Jami’a su janye yajin aiki
Malaman sun tsunduma yajin aikin ne sakamakon gaza biyan su wasu haƙƙoƙinsu.

Gwamnatin Jihar Sakkwato, ta buƙaci malaman jami’ar jihar da suka shiga yajin aiki da su koma bakin aiki don ci gaban ilimi a jihar.
Kwamishinan Ilimi Mai Zurfi, Farfesa Isah Muhammad Maishanu ne, ya bayyana haka a taron manema labarai da ya kira a ranar Juma’a, kwana ɗaya bayan da malaman suka fara yajin aiki saboda rashin biyansu haƙƙoƙinsu.
- An ga jinjirin watan Ramadan a Saudiyya
- Sojoji sun kama shugaban ’yan bindiga, Kachallah Hassan Nabamamu a Zamfara
Ya ce: “Muna kira ga malaman da su sake tunani kan matakin da suka dauka. Kada su bari siyasa ko wasu da ba su da kishin jiha su yi amfani da su wajen hana ci gaban ilimi.
“Mu na mutunta su, kuma muna fatan su koma bakin aikinsu.”
Ya ƙara da cewa gwamnati ta ɗauki ƙorafe-ƙorafen malaman da muhimmanci, don haka an kafa kwamiti da ke tattaunawa da ɓangarorin da abin ya shafa kan matsalar rashin biyan su kaso 25 da 35 na albashinsu.
Dangane da matsalar gidajen malamai da suka fara lalacewa, kwamishinan ya bayyana cewa gwamnati ta tura injiniyoyi domin tantance halin da suke ciki da nufin gyara su.
Duk da haka, wasu masu sharhi a Sakkwato na ganin cewa gwamnati ba ta ɗauki matakan da suka dace don warware matsalar malaman ba.
A cewarsu, maimakon ɗaukar matakin magance matsalolin, gwamnati kawai tana bayar da umarni ne wanda ba ya taimakawa wajen yin sulhu.