Gwamnatin Sakkwato ta yaye jami’an tsaro 1,550
Gwamnan Jihar Ekiti, Mista Biodun Oyebanji ne ya ƙaddamar da rukuni na biyu na dakarun a matsayin babban baƙo a wurin bikin ya nuna farin cikin yadda Gwamnan Sakkwato ya ba shi damar zuwa jihar a karon farko.
Gwamnatin Jihar Sakkwato ta yaye jami’an tsaro na Marshall su 1,550 a yunƙurinta na inganta harkar tsaro da kare rayukan mutane a jihar.
Jami’an suna da rukuni guda huɗu, kula da muhalli da tsaro da sirri da harkokin kula da ababen hawa, an ba su horo na mako takwas, inda a karon na farko aka sanya mata a cikinsu.
- Kuɗaɗen ajiyar Najeriya a waje sun ƙaru zuwa biliyan $52.73
- 2027: A guji tikitin Gwamna masu addini ɗaya — Sheikh Maraya
Gwamnan Jihar Ekiti, Mista Biodun Oyebanji ne ya ƙaddamar da rukuni na biyu na dakarun a matsayin babban baƙo a wurin bikin ya nuna farin cikin yadda Gwamnan Sakkwato ya ba shi damar zuwa jihar a karon farko.
A cewarsa bayar da horo ga jami’an Marshal ya bayyana yadda ake son samar da zaman lafiya da tsaro da haɗin kan kasa.
Gwamnan Sakkwato, Dakta Ahmad Aliyu a wurin ya ba da tabbacin samar da duk wani abu da jami’an ke buƙata kama da ababen hawa da na’urar magana da duk wani abu da zai taimakawa aikinsu domin samun nasarar aikin, za a kuma tura dukkan jami’an a ƙananan hukumomi a 23 kowane jami’i za a aje shi a mahaifarsa domin ba da gudunmuwa.
Gwamnan ya nemi jami’an su haɗa kai da jami’an tsaro na kowane ɓangare domin ganin an tsare rayukan ’yan ƙasa.
Gwamnan ya ce, “Duk abubuwan nan da muke yi don ƙara ƙarfafa jami’an tsaronmu ne, ’yan uwana jama’ar Sakkwato kamar yadda kuka sani tun sanda Allah Ya ba mu wannan jagoranci mun cigaba da yin abubuwa da dama domin ganin an samar da tsaro, mun yi duk abin da ya kamata mu yi, iyakar yinmu domin ganin tsaro ya samu”.
“Harkar tsaro ba ta tabbata sai da taimakon kowa ya zama wajibi a gare mu zama wuri ɗaya don samar da tabbataccen tsaro a faɗin jihar Sakkwato,” cewar Gwamnan Sakkwato.

