Gwamnatin Sakkwato za ta bayar da tallafin kashi 70 kan kudin taki

Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal da Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar sun kaddamar da sayar da takin zamani na bana a jihar, inda Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta bayar da tallafin kashi 70 cikin 100 kan kudin takin a bana.Lokacin da yake jawabi a wajen kaddamar da sayar […]

Gwamnatin Sakkwato za ta bayar da tallafin kashi 70 kan kudin taki
Gwamnatin Sakkwato za ta bayar da tallafin kashi 70 kan kudin taki

Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal da Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar sun kaddamar da sayar da takin zamani na bana a jihar, inda Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta bayar da tallafin kashi 70 cikin 100 kan kudin takin a bana.
Lokacin da yake jawabi a wajen kaddamar da sayar da takin wanda aka gudanar a karamar Hukumar Silame, Gwamna Tambuwal ya bayar da sanarwar cewa gwamnatin za ta bayar da tallafin kashi 70 cikin 100 kan kudin takin domin inganta noma a jihar.
 Ya ce, gwamnatin ta sayo nau’o’i uku na takin da suka hada da yuriya da NPK da SSP, “A bana gwamnati ta sayo Yuriya a kan Naira6,859, kuma za ta sayar wa manoma a kan Naira 2,300; sai NPK ta sayo shi a kan Naira 6,400, za a sayar da shi ga manoma a kan Naira 2,200, yayin da SSP shi ma aka sayo shi a kan Naira 6,400 kuma za a sayar da shi a kan Naira 2,100,” inji Gwamnan.
Gwamna Tambuwal ya kara da cewa gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba a kokarinta na inganta harkokin noma a jihar.
Gwamnan ya ce gwamnatin ta kuma sayo buhunan irin shinkafa dubu 19 da 620 masu nauyin kilo 50 domin rarrabawa ga manoma domin noman rani. “Kuma mun samo ingantaccen iin albasa da latos domin rarraba wa manoman kayan lambu da suke kananan hukumomin Goronyo da Rabah da Wurno da Kware da Tambuwal da Wamakko da Silame da Kebbe da Sakkwato ta Arewa da kuma Shagari,” inji shi.
Ya ce gwamnatin za ta ci gaba da inganta hanyar kula da ruwa musamman a manyan madatsu biyu da ke jihar domin magance ambaliya da illar da take yi, kuma a lokaci guda ta inganta noman rani.
Kimanin tan dubu tara na takin zamani gwamnatin jihar ta sayo domin rarrabawa a daminar bana.

Zazzaɓin Lassa ya kashe mutum 214 a Najeriya — NCDC

An kama masu garkuwa da mutane a Borno 

Rikicin ya kunno kai a Hukumar Alhazan Jihar Delta

Sojoji sun ceto mutane 5 da ISWAP ta sace a Harin Ngoshe