Gwamnatin Sakkwato za ta fara biyan Malaman Zaure albashi

Gwamnatin Jihar Sakkwato za ta sanya Malaman Zaure da ke karantar da addinin Musulunci cikin tsarin  albashi na wata-wata don su hade da takwarorinsu masu koyar da ilimin boko a jihar. Kwamishinan Ilimi na Jihar Dokta Muhammad Jabbi Kilgori ne ya bayyana haka a wurin bikin yaye dalibai 163 da suka sauke karatun Alkur’ani Mai […]

Gwamnatin Sakkwato za ta fara biyan Malaman Zaure albashi

Gwamnatin Jihar Sakkwato za ta sanya Malaman Zaure da ke karantar da addinin Musulunci cikin tsarin  albashi na wata-wata don su hade da takwarorinsu masu koyar da ilimin boko a jihar.

Kwamishinan Ilimi na Jihar Dokta Muhammad Jabbi Kilgori ne ya bayyana haka a wurin bikin yaye dalibai 163 da suka sauke karatun Alkur’ani Mai girma kuma suka koyi  sana’o’i daban-daban don dogaro da kai da kuma 13 da suka haddace Alkur’ani Mai girma da Makaranatar Dirasatul Islamiyya Wal kur’aniyya Wal Arabiya Li-Sheikh Malami Mai Lafiya ta shirya a ranar Asabar da ta gabata a Sakkwato.

Kwamishinan ya ce “Shigowa da Malaman Zauren wata hanya ce ta rage yawan bara da almajirai ke yi da kuma taimakawa al’ummarmu su samu ilimin addin da na zamani a lokaci daya. Kowane malami za a rika biyansa albashinsa daidai da iliminsa wannan magana a tattauna ta a zaman Majalisar koli ta Ilimi ta kasa kuma an amince da ita, a nan matakin jiha da zarar an kammala tantance malaman za su fara cin wannan gajiya.’

A jawabin Gwamnan Jihar Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya jinjina wa makarantar kan namijin kokari da take yi na bai wa dalibai yara da mata ilimim addini da na sana’a a lokaci daya. Ya ce wannan abin yabo ne kuma akwai bukatar a samu karuwar irin wannan makaratar a Najeriya, ganin ilimi ba sana’a kan jefa wadansu a cikin aikin rashin gaskiya.

Gwamna Tambuwal wanda Kwamishinan Harkokin Addini, Alhaji Mani Maishinko Katami ya wakilta ya ce hukumar kula da kanana da matsaikatan sana’o’i ta jihar za ta fito da wasu makarantun koyon sana’a a yankunan Sakkwato uku domin a kara samun yawaitar masu irin wadannan sana’o’i da makaratar ta koyar da dalibanta. Ya ce akwai bukatar a kara inganta wadannan sana’o’i su dace da zamani kuma su rika gogayya da takwarorinsu na sauran kasar nan.

Shugaban Makarantar, Malam Mujjitaba Shehu Garge ya ce makaratar ta faro ne a shekarar 2003 tare da dalibai 13 da malamai 4 , inda alke karatu da marece, amma yanzu tana da dalibai 6000 da bangaren Islamiyya da sakandare tare da koyon sana’o’i da kuma gefen Malaman Zaure.

Malam Mujjitaba ya ce makarantar tana da matsalolin da suka hada da rashin wuri na dindindin da injunan zamani na aiki da mai ba da wutar lantarki da saurasu.

Makaratar tana koyar da kayan kwalliya na mata da yin bonbita da turare da magungunan kashe kwari da sauransu.