Gwamnatin Sakkwato za ta kashe fiye da Naira biliyan daya don inganta noma
Gwamnatin Jihar Sakkwato tare da hadin gwiwar Bankin Zenith za su kashe sama da Naira biliyan daya ga manoman jihar a kokarinta na inganta harkar noman rani da damina a jihar, inda za ta saye shinkafa da tumatir din da suka noma.Kwamishinan Ma’adinai na Jihar Alhaji dahiru Maishanu ya fadi haka a lokacin da yake […]
Gwamnatin Jihar Sakkwato tare da hadin gwiwar Bankin Zenith za su kashe sama da Naira biliyan daya ga manoman jihar a kokarinta na inganta harkar noman rani da damina a jihar, inda za ta saye shinkafa da tumatir din da suka noma.
Kwamishinan Ma’adinai na Jihar Alhaji dahiru Maishanu ya fadi haka a lokacin da yake yi wa manema labarai bayani bayan zaman Majalisar Zartarwar Jihar a shekaranjiya Laraba.
Kwamishinan ya ce majalisar ta yanke shawarar fadadawa da gyara makarantar sakandaren ’ya’yan sojoji da ke jihar, kan Naira miliyan 120.
Kwamishina Watsa Labarai na Jihar Nasir danladi Bako ya ce majalisar ta zartar da sake zagaye gidan gwamnatin jihar inda za a yi masa ginin zamani tare da samar da wuraren a jiye motoci, ganin ginin da
ke tsaye a yanzu ya fi shekara 30 kan Naira miliyan 772. Ya ce kuma za a gyara gidajen malamai da wasu ajujuwa da ke makarantar Nagarta.
Sai Kwamishinan Lafiya na Jihar Alhaji Ahmad Aliyu wanda ya ambaci hanyoyi biyu da aka dade da bayar da aikinsu amma har yanzu ba a kammala aikinsu ba bisa wasu dalilai, inda ya ce a yanzu majalisar ta kara kudi ga ’yan kwangilar saboda su kare hanyoyin Sakkwato zuwa Illela da Durbawa zuwa Maikujera.