Gwamnatin Sakkwato za ta kashe N6.7bn wajen ciyarwar Azumi
Kowanne mutum zai samu buhun shinkafa, da na gero da kuma N5,000.
Gwamnatin Sakkwato ta ce za ta kashe Naira biliyan 6.7 domin ciyar da marayu da talakawa a watan Azumi na Ramadan.
A cewar gwamnatin, ciyarwar ta haɗa da rabon hatsi da kuma dafaffen abinci, wanda za a raba a cibiyoyin rabon abinci da ke faɗin jihar.
- Ban mayar da hankali kan ɗora wa gwamnatin da ta shuɗe laifi ba —Tinubu
- Sojin Nijar za su saki Bazoum
Gwamna Ahmed Aliyu ne ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da rabon hatsin ga marayu da marasa ƙarfi 18,400 a faɗin jihar, inda ya ce kowannensu zai samu buhun shinkafa, da na gero da kuma N5,000.
A nasa bangaren Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya gode wa Gwamnan bisa ƙoƙarinsa na ɗabbaka wannan shirin, tare da tabbatar masa da goyon bayansa wajen inganta rayuwar al’umma.