Gwamnatin Sakkwato za ta sanya wa asibitoci 244 kayan aiki

Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya ce gwamnatinsa za ta sanya wa kananan asibitoci a matakin farko 244 da gwamnatin da ya gada ta gina kayan aiki dominn inganta harkokin kiwon lafiya a jihar. Gwamna Aminu Tambuwal ya bayyana haka ne a fadar gwamnatin jihar wurin taron sanya hannun kan yarjejeniya fahimtar juna a […]

Gwamnatin Sakkwato za ta sanya wa asibitoci 244 kayan aiki
Gwamnatin Sakkwato za ta sanya wa asibitoci 244 kayan aiki

Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya ce gwamnatinsa za ta sanya wa kananan asibitoci a matakin farko 244 da gwamnatin da ya gada ta gina kayan aiki dominn inganta harkokin kiwon lafiya a jihar.
 Gwamna Aminu Tambuwal ya bayyana haka ne a fadar gwamnatin jihar wurin taron sanya hannun kan yarjejeniya fahimtar juna a tsaknin gwamnatinsa da Hukumar UNICEF da bayar da ofishi na yankin Sakkwato da Kebbi da Zamfara ga hukumar.
Binciken Aminiya ya gano mafi yawan asibitocin da aka gina, ba kayan aiki a cikinsu ginawar ce kawai aka yi, ciki har da babban asibitin da aka gina a garin Tsamiya a karamar Hukumar Tureta domin kwantar da marasa lafiya, amma aka yi bikin bude shi ba tare da an sanya masa kayan aiki ba, a zamanin gwamnatin da ta gabata.
Gwamnan ya ce “A bana mun samu nasarar cimma burinmu na yawan yaran da muke son su shiga makaranta, kuma sanya hannu a wannan yarjejeniyar bukata ce ta yadda za a inganta rayuwar yaran da suke makarata domin bunkasa karatunsu a kowane fanni. Ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen nemo hukumomin da suke son ci gaba don su zo mu ciyar da jihar nan gaba a kowane bangare na rayuwa.”
Tun farko wakiliyar Hukumar UNICEF a Najeriya Misis Jean Gough ta roki gwamnatin jihar ta kaddamar da shirin bayar da abinci ga ’yan firamare a duk fadin jihar.
 Ta ce yin wannan hakan zai karfafa wa iyaye da yaran su rika sanya su a makaranta tareb da zuwa makarantar ta yadda hakan zai rage yawon banza a tsakanin yara. “Za mu karfafa wa gwamnatin Sakkwato ta fannin ilimi domin a samu biyan bukatar da ta sanya a gaba wanda ya sanya ta fito da dokar ta-baci a fannin ilimi, koyaushe hukumarmu a shirye take ta taimaki yara a duk bangarorin rayuwarsu,” inji Gough.

Zazzaɓin Lassa ya kashe mutum 214 a Najeriya — NCDC

An kama masu garkuwa da mutane a Borno 

Rikicin ya kunno kai a Hukumar Alhazan Jihar Delta

Sojoji sun ceto mutane 5 da ISWAP ta sace a Harin Ngoshe