Gwamnatin Sakkwato za ta tallafa wa mata 2,440 don bunkasa kiwon awaki

Gwamnatin jihar Sakkwato tana shirin fito da tsarin bunkasa kiwon awaki. Kwamishinan Kula da Lafiyar Dabbobi da Kiwon Kifi na Jihar, Farfesa Abdulkadir Junaid,  ya ce “A Jihar Sakkwato, yawan awakin da ake da su na kiwo na raguwa; mutane suna cinye su ba a samar da madadinsu.” Saboda haka ya ce Gwamnatin Jihar Sakkwato […]

Gwamnatin Sakkwato za ta tallafa wa mata 2,440 don bunkasa kiwon awaki

Gwamnatin jihar Sakkwato tana shirin fito da tsarin bunkasa kiwon awaki. Kwamishinan Kula da Lafiyar Dabbobi da Kiwon Kifi na Jihar, Farfesa Abdulkadir Junaid,  ya ce “A Jihar Sakkwato, yawan awakin da ake da su na kiwo na raguwa; mutane suna cinye su ba a samar da madadinsu.”

Saboda haka ya ce Gwamnatin Jihar Sakkwato ta shirya bunkasa kiwonsu “Muna da kudirin sayo awaki masu yawa mu raba su ga zawarawa a dukkan mazabu 244 da ke Jihar Sakkwato. Kowace mace za mu ba ta guda biyar da abincinsu; mu gani a cikin shekara biyu ko za su iya ninkawa sau biyu,” inji shi.

Ya ce shirin ba wai kawai zai kara yawan awakin ba ne, har da samar da aikin yi ga wadanda za su ci gajiyar shirin.

“Kudirinmu a bai wa mata 10 daga kowace mazaba 244 da ke kananan hukumomi 23 na Jihar Sakkwato. Da zarar muka yi haka mun samar musu da kananan sana’o’in aiwatarwa,” inji shi.

Ya kara da cewar ma’aikatarsa ta riga ta cimma matsayar shiga cikin wannan ci gaban “Muna kan shirin yin matsayar mayar da abin kasuwanci da zai samar da kudin shiga  ga gwamnati. Kuma su ma makiyayan za su ji dadinsa,” inji Kwamishinan.