Gwamnatin Saudiyya ta karyata batun tone kushewar Annabi

Gwamnatin kasar Saudiyya ta karyata labarin da jaridar The Independent ta bada a ranar Litinin din makon jiya kuma aka rika watsawa a kafofin sadarwa na intenet cewa tana shirin tone kushewar Annabi (SAW) don mayar da ita wani wuri na daban daga masallacinsa da ke Madina.Jaridar Saudi Gazzet ta ruwaito Kakakin Fadar Sarkin Saudiyya […]

Gwamnatin Saudiyya ta karyata batun tone kushewar Annabi
Gwamnatin Saudiyya ta karyata batun tone kushewar Annabi

Gwamnatin kasar Saudiyya ta karyata labarin da jaridar The Independent ta bada a ranar Litinin din makon jiya kuma aka rika watsawa a kafofin sadarwa na intenet cewa tana shirin tone kushewar Annabi (SAW) don mayar da ita wani wuri na daban daga masallacinsa da ke Madina.
Jaridar Saudi Gazzet ta ruwaito Kakakin Fadar Sarkin Saudiyya Ahmad Al-Mansouri, yana cewa, Hukumar Kula da Masallatan Haramomin Biyu rahoton da kafafen watsa labarai suka bayar game da kushewar Annabi Muhammad ra’ayi ne na wani mai bincike amma babu ruwan masarautar da shi.
“Abin da ake yayatawa a kafafen labarai game da kushewar Annabi (SAW) da ke cikin masallacinsa ya shafi wani bincike ne da wani ya yi. Ba ya wakiltar ra’ayin mahukuntan kasar kuma ba umarni na gwamnati ba, wadda take tsaye wajen yin hidima ga masallatan biyu mafiya daraja a duniya tare da ci gaba da kare martabarsu,” inji Ahmad Al-Mansouri.
Jaridar The Independent ta bada rahoto a ranar Litinin da ta gabata inda ta yi zargin ana shirin tone kushewar Annabi (SAW). Rahoton dai ya ginu ne kan wani bincike da wani malamin makaranta dan Saudiyya mai suna Ali Al-Shabal ya gudanar, inda ya fito a wata takarda da aka buga da sunan mahukuntan kasar. A cikin binciken marubucinsa ya kawo shawarar a tone kusherwar a maida ta Baki’a, bisa abin da ya kira hana mutane bauta mata, amma babban kwamitin kula da fadada masallatan Harami ya yi watsi da shawarar da kuma shawarar a raba kushewar da masallacin ta koma gefe.
Kakakin masarautar ya ce: “Masu bincike da sauran kafafen watsa labarai, su guji buga bayanan da za su jawo rudani da ingiza tashin hankali. Maimakon haka su rika bayar da bayanan da za su kasance na hikima da bayyana gaskiya ba tare da kara gishiri ba, musamman kana bin da ya shafi masallatan biyu masu alfarma.”