Gwamnatin Shugaba Jonathan ta bar baya da kura

Mu fara da cin hanci da rashawa. Cin hanci da rashawa, matsala ce da ta yi kamari a kasashe da dama na duniya, tare da janyo cikas ga yadda ake gudanar da aiyukan al’umma. An dade ana zargin manyan jami’an gwamnati da hada baki da kamfanoni ko bankuna domin sace dukiyar da aka ware don […]

Gwamnatin Shugaba Jonathan ta bar baya da kura
Gwamnatin Shugaba Jonathan ta bar baya da kura

Mu fara da cin hanci da rashawa. Cin hanci da rashawa, matsala ce da ta yi kamari a kasashe da dama na duniya, tare da janyo cikas ga yadda ake gudanar da aiyukan al’umma.

An dade ana zargin manyan jami’an gwamnati da hada baki da kamfanoni ko bankuna domin sace dukiyar da aka ware don raya kasa.
Alal misali, a wani jawabi da ya gabatar a gaban Majalisar Dokoki ta Amurka, a 2010 tsohon Shugaban hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annati, Malam Nuhu Ribadu, ya bayyana cewa abin da aka sace a kasar daga 1960 zuwa 1999, ya kai dalar Amurka biliyan 440. Malam Nuhu Ribadu ya ce, yawan wadannan kudade sun ribanya wadanda aka kashe a gagarumin shirin gina kasahen Turai bayan yakin duniya na biyu har sau shida. Sannan masana na ganin cewa, kudaden da aka yi sama da fadi da su daga 1999, bayan kafuwar mulkin dimokradiyya a Najeriyar ya zuwa yanzu, sun ninka wadannan alkaluma da aka ambata.
Sai dai matsalar ba wai ta tsaya ga bangaren hukumomi ba ne kawai, su ma jama’ar gari na yin amfani da damar su wajen aikata cin hanci da rashawar. Ban manta da badakalar kwamitin Majalisa na Faruku Lawal ba.Inda har Majilisa ta dakatar da shi saboda zargin amsar na goro. Majalisar ta kuma sake duba matsayar da ta dauka a ranar 24 ga watan Afrilu, na wanke kamfanin Zenon Petroleum and Gas and Synopsis Enterprises daga hannu a badakalar tallafin man. Tun da farko an zargi Zenon Petroleum and Gas, mallakin Femi Otedola da karbar dala 232,975,385.13 domin shigowa da man fetur, sai dai ba su shigo da man ba.
Mu koma bayan kammala zaben inda nasarar cinye zaben Shugaba Jonathan ya kawo tarzoma a wasu jahohin Arewa. A ranar 11 ga watan Mayu ne 2011 gwamnatin Najeriya ta kafa kwamitin da zai binciki tashe-tashen hankulan da suka faru a wasu jihohin Arewacin kasar, biyo bayan zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan Afrilu. Kwamitin, mai mambobi 22 ya kasance karkashin jagorancin Sheikh Ahmed Lemu, kuma tsohon jojin kotun koli, mai shari’a Samson Uwaifo ne mataimakinsa. Kwamitin ya mika rahotansa inda ya yi kira ga Mahukuntan kasar da ayi hattara ‘yan kasa na cikin zafin da radadi na barazanar tsaro da talauci, wanda haka ka iya jefa kasar cikin Juyin juya hali.
Ranar da ba zan taba mantawa da ita ba ita ce ranar da muka wayi gari da ita da goron sabuwar shekara ranar 01/01/2012 gwamnatin Shugaba Jonathan ta ayyana janye tallafin man fetur, a duk arzikin kasarmu shi ka dai ne talaka ke amfanuwa da shi. Gwamnatin ta yi kiyasin cewa za ta samu karin kudaden da suka kai dala biliyan 8 daga janye tallafin, kuma ta ce za ta yi amfani da su ne wurin aiyukan ci gaban kasa.
Najeriya na daya daga cikin kasashen da ke kan gaba wajen samar da danyan man fetur, amma tana shigo da man da take amfani da shi ne daga waje, sakamakon rashin ingantattun matatun mai da kuma tashe-tashen hankula.
A ranar 2/ 08/2011 aka fara rantsar da kwamiti da zai sasanta da masu ta da kayar baya abin kamar gaske, a gefe daya kuwa an gano kafar ungulu gwamnatin take yi ,wanda har izuwa yau dinnan Allah kadai ya san adadin bama-bamai da suka tashi da dimbin hasarar dukiya da rasa rayuka da aka yi wanda kiyasin rai sama da dubu ashirin sun mutu.
Ranar da aka shiga yajin aikin a makarantun Jami’oi a kasar nan an sha wuya, tabbas gwamnati ta yi kunnen uwar shegu da abin. Sai da aka kai ruwa rana kimanin wata tara dalibai suka kwashe a zaune a gidajensu ba uhum ba a’a.
‘Yan matan Chibok tab! Da farko ma gwamnatin ba ta yarda an sace su ba.Sai dai kash ta baro hannun agogo a baya domin ta yi amai ta lashe ta kuma kasa tabuka komai a kai tun a watan Aprilun bara babu labari. Labari mai dadin ji shi ne na bayan nan, na ceto ‘yan mata da manyan mata. Daga nan Ina addu’ar Allah ya sa duk wahalhalun da aka sha a baya su zama tarihi. Janar Muhammadu Buhari ya kasance jagora nagari ga kasarmu. Ya kai mu tudun mun tsira kamar yadda kowane dan kasa ya yi masa kyakkyawan sanin halaye na kwarai. Fata nagari lamiri. Allah ya sa kama aiki da sabuwar gwamnati ta yi,ta fuskanci kalubalen da ke gabanta a cikin sa’a.
Daga Hafizu Balarabe Gusau
07035304499