Gwamnatin sojin Burkina Faso ta ce ta sha daƙile yunƙurin hargitsa ƙasar
Ana zargin Laftanar Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba, wanda aka hambarar da gwamnatinsa a shekarar 2022 ya jagoranci ɓangaren soji na wannan mummmunan shirin
Gwamnatin sojin Burkina Faso ta ce ta daƙile yunƙuri da dama na kawo ruɗani a ƙasar a ƙarƙashin jagorancin wani tsohon babban hafsan soji, wanda ya taɓa kifar da gwamnati a ƙasar ta yammacin nahiyar Afrika.
Ministan tsaro na ƙasar, Mahamadou Sana, wanda ya bayyana haka a wata sanarwa da aka karanta a kafar talabijin a daren Litinin ya ce Laftanar Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba, wanda aka hambarar da gwamnatinsa a shekarar 2022 ya jagoranci ɓangaren soji na wannan mummmunan shirin.
Sana ya ce mmutane da dama ne aka kama sakamakon nasaba da wannan shiri, cikin su har da Ahmed Kinda, wani tsohon kwamandan runduna ta musamman.
Damiba ya yi juyin mulki a watan Janairun shekarar 2022, inda ya kifar da gwamnatin zaɓaɓɓen shugaban ƙasar, Roch Marc Christian Kabore.
- Za a kai shugaban ’yan sanda kotu kan kudin otel N625m
- Yara 2,300 da mata 145 ke mutuwa kullum a Najeriya —NPHCDA
Watanni 8 kawai ya yi a kan karagar mulki, shi ma aka kifar da gwamnatinsa, a wani juyin mulki da kyaftin ɗin soja mai shekaru 30, Ibrahim Traore.
A ƙarƙashin mulkin Traore, Burkina Faso ta juya wa tsohuwar uwargijiyarta, wato Faransa, kana ta sha ganin bayan matsalar ta’addanci da ta yi da ta addabi ƙasar, wadda ta samo asali daga Mali a shekarar 2015.
Tuni Burkina Faso ta koma ga Rasha don neman taimakon soji, kana ta ƙarfafa dangantaka da Iran, Turkiyya da kuma Nijar da Mali.