Gwamnatin sojin Nijar ta janye jakadan kasar a Ivory Coast

Sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar sun janye jakadan kasarsu a Ivory Coast saboda kalaman goyon bayan kai wa Nijar hari

Gwamnatin sojin Nijar ta janye jakadan kasar a Ivory Coast

Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar sun janye jakadan kasar a Abidjan, babban birnin Ivory Coast a ranar Litinin, saboda kalaman shugaban kasar, Alassane Ouattara, wadanda suka ce suna nuna alamta goyon baya ga batun kai wa Nijar farmaki.

Gwamnatin soji Nijar din ta caccaki Outarra a game da kalaman nuna goyon baya ga abin da ta ce saba wa doka ce tare da rashin hankali, suna mai cewa ya zake dayawa.

Bayan dawowarsa  daga taron kungiyar raya tattalin arzikin yammacin Afrika ta ECOWAS da aka yi a Abbuja, babban birnin Najeriya, Ouattara ya ce shugabannin kasashen kungiyar sun amince a farmaki a kan masu juyin mulki nan ba da jimawa ba.

Ya ce Ivory Coast za  ta bada gudummawar bataliyar sojoji mai dakaru tsakanin 850 zuwa 1,100 don su hade da na Najeriya da Jamhuriya Benin.

Wata sanarwar da gwamnatin sojin Nijar ta fitar ta ce barazanar da  ECOWAS ke yi na nuni da cewa  akwai wata kasa ta waje da ke kokarin amfani da ita, sai dai ba ta bayyana ko wace kasa ba ce.

Sanarwar ta yi watsi da kalaman Ouattara, wanda ta ce sun wuce abin da za a dauka a matsayin na ECOWAS ne, saboda haka tana mai janye jakadanta na Abidjan daga kasar.

A makon da ya gabata, ECOWAS ta jaddada matsayinta na kare dimokaradiyya, inda nuna aniyarta ta maido da haambaraarren shugaba Mohamed Bazoum ba tare da karin bayani a kan yadda za ta yi amfani da karfi  ba.