Gwamnatin Sojin Nijar ta tsige shugaban ’yan sandan Yamai

Mahaman ya gargadi masu zaman dirshan a harabar sansanin sojan Faransa.

Gwamnatin Sojin Nijar ta tsige shugaban ’yan sandan Yamai

Gwamnatin Soji a Jamhuriyar Nijar ta tsige Shugaban hukumar ‘yan sandan birnin Yamai, Kwanturola-Janar Abdoulsalam Mahaman.

Wannan dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan da ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda wasu daga cikin masu zanga-zangar nuna bukatar ficewar sojan Faransa ke wuce gona da iri har ma da yin fatali da doka.

A jiya Litinin ne takardar tsige Kwanturola-Janar Abdoulsalam Mahaman dauke da sa hannun Ministan Cikin Gida, Janar Mohamed Toumba ta fara karade kafafen sada zumunta, wacce wata majiyar sabbin hukumomin na Nijar ta tabbatar wa Muryar Amurka da sahihancinta.

A ranar Larabar da ta gabata ne Mahaman ya gargadi masu zaman dirshan a harabar sansanin sojan Faransa da ke dab da filin jirgin saman Yamai da su koma gefen titi domin bai wa masu ababen hawa damar kai da kawo ba tare da wata tsangwama ba.

Ya kuma nuna rashin jin dadinsa kan yadda wasu daga cikin wadanan mutane ke uzzurawa masu ababen hawa da suke tilasta cire belt ga masu motoci ko hular kwano ga masu babura.

Haka kuma, Mahaman ya sanar cewa, suna da bayanan cin zarafin mutane a wannan wuri ciki kuwa har da yi wa mata fyade saboda haka ya bukaci hadin kan jagororin zanga-zangar domin tabbatar da doka da oda.

Ba a dai yi bayani a hukunce kan dalilan daukan wannan mataki ba, to amma a ra’ayin wani dan farar hula na gamayyar Reseau Esperance Bachar Maman za ta yiwu abin na da nasaba da furucin da Shugaban ‘yan sandan na Yamai ya yi game da abubuwan da ke wakana a harabar Escadrille.

Da ma tun a ranar ziyarar ta Mahaman, daya daga cikin jagororin wannan zanga-zanga Gamatche Mahamadou ya rubuta a shafinsa na facebook cewa, kalaman na Shugaban ‘yan sandan birnin Yamai zagon kasa ne da ya kitsa takanas da nufin karfafa gwiwa ga mukarabban tsohuwar gwamnati, saboda haka ake ganin rubutunsa tamkar shawara ce ya bai wa hukumomin mulkin soja.

Tun a washe garin juyin mulki na 26 ga watan Yuli ne matasa suka kaddamar da ayyukan binciken motoci da ababen hawa a titunan birnin Yamai, galibi da dare da nufin dakile yunkurin dukkan wata aika-aika.

Haka kuma, irin wannan aiki ke gudana daga ran 1 ga watan Satumba a harabar sansanin sojan Faransa, sai dai wasu mazaunan birnin Yamai sun koka kan yadda wasu daga cikin masu aikin binciken ke wuce gona da iri, wasu ma na ganin tamkar masu zanga-zangar na shiga hurumin jami’an tsaro.

Bin diddigi: Gaskiyar batun kai hari a Bankin CBN

NAJERIYA A YAU: Lakurawa muka kai wa hari a Sakkwato —Sojoji

Manyan alhinin Najeriya a 2024

’Yan sanda sun kama waɗanda suka shirya rikicin ‘yan daba a Kano