Sudan ta kaddamar da sauye-sauye a kundin tsarin mulki
Sauye-sauyen za su ba shi cikakkiyar damar naɗawa da cire duk wanda yake buƙata ciki har da Firaminista
Shugaban mulkin sojin Sudan Abdel Fattah al-burhan na shirin faɗaɗa madafan ikonsa, a yayin da ya gabatar da buƙatar sauye-sauye a cikin kundin tsarin mulkin ƙasar.
Sauye-sauyen da shuagaban mulkin sojin na Sudan ya buƙaci a yi, zai ba shi cikakkiyar damar naɗawa da cire duk wanda yake buƙata ciki har da Firaminista a kasar.
Haka nan sauyin zai ba da damar ƙara adadin mambobin zartaswar ƙasar daga biyar zuwa tara.
Sannan mutane ukun da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar wanzar da zaman lafiya ta juba za su ci gaba da zama matsayinsu a yayin da shi kuma zai naɗa wasu mambobi shifa.
Batun gyaran da wasu ’yan siyasa da ke da alaƙa da sosjojin ƙasar suka shirya, ya samu ne bayan da aka buƙaci a gudanar da kwaskwarimar yarjejeniyar da aka shirya ta shekarar 2019.
Sauye-sauyen zai kawar da duk wani tsari na ƙungiyar ’yancin samar da sauyi da kuma dakarun ɗaukin gaggawa ta RSF, a yayin da za a bar wakilan da suka rattaba hanu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta juba a kan aikinsu.
Al-Burhan ya ba da wannan sanarwar sauye-sauyen ne a yayin wani bikin mata da gudana a Omdurman a wannan mako.