Gwamnatin ta bullo da sabuwar dokar yaki da ta’addanci, Inji Atone-Janar

  Atone Janar kuma Ministan Shari’a, Babban Lauya Abubakar Malami ya bayyana wata sabuwar doka da ke yaki da ta’addanci a kasa.   Ministan Shari’ar ya ce sabuwar dokar mai lakabin: “Kudurin Haramcin Ta’addanci da Yakar shi” zai maye gurbin kudurin yaki da ta’addanci na shekarar 2011 wanda aka yi wa gyaran fuska a shekarar […]

Gwamnatin ta bullo da sabuwar dokar yaki da ta’addanci, Inji Atone-Janar

 
Atone Janar kuma Ministan Shari’a, Babban Lauya Abubakar Malami ya bayyana wata sabuwar doka da ke yaki da ta’addanci a kasa.
 
Ministan Shari’ar ya ce sabuwar dokar mai lakabin: “Kudurin Haramcin Ta’addanci da Yakar shi” zai maye gurbin kudurin yaki da ta’addanci na shekarar 2011 wanda aka yi wa gyaran fuska a shekarar 2013.
 
Da yake jawabi a bude taron kara wa juna sani na yanki kan tattara bayanai a mahangar yaki da ta’adanci wanda aka gudanar a Abuja jiya, Malami ya  ce idan majalisa ta amince da kudurin, dokar za ta kara kyautata dangantakar jami’an tsaro da jami’an tattara bayanan sirri da ma’aikatan gidan yari da sauran jami’an tsaro na kasa baki daya.
 
Malami wanda Daraktan Gabatar da kara na gwamnati, Mohammed Etsu ya wakilta ya ce dokar ta kara fadada ma’anar  daukar nauyin ta’addanci da kuma hukuncin da aka tanada ga ’yan ta’adda da wadanda ke basu kudi.