Gwamnatin Taliban ta ba da umarnin rufe dukkan shagunan gyaran jiki a Afghanistan

Mata da dama dai a kasar na da irin wadannan shagunan

Gwamnatin Taliban ta ba da umarnin rufe dukkan shagunan gyaran jiki a Afghanistan

Shagon gyaran jiki a Afghanistan

Gwamnatin Taliban da ke Afghanistan ta bayar da umarnin rufe dukkan shagunan gyaran jiki na mata da ke fadin kasar.

Kafafen yada labaran kasar sun rawaito wata sabuwar doka da gwamnatin kasar ta fitar na cewa, “Ba a yi wani karin bayani kan makasudin daukar wannan matakin ba. Lasisin da shagunan ke bukata domin yin aiki za su kare a wata mai zuwa.”

Shagunan gyaran jiki dai na daya daga cikin manyan hanyoyin da matan kasar ke samun kudaden shiga, inda wasu matan ma su ne sauran iyalansu suka daogara da su.

Tun lokacin da ta kwaci mulki a watan Agustan shekara ta 2021, Taliban ta yi alkawarin kiyaye hakkokin mata a kasar.

Sai dai tun daga lokacin, an dakatar da mata daga sana’o’i da ayyuka da dama.

Hatta makarantun sakadare da jami’o’in kasar sai da gwamnatin ta hana mata zuwansu.

Ba kasafai dai ake bin dokokin gwamnatin sau da kafa ba. Ko a Kabul, babban birnin kasar, mata da dama ne ke yawo ba tare da sun rufe fuskokinsu ba, sabanin umarnin Taliban.

Kazalika, makarantu masu zaman kansu da dama sun ci gaba da iimantar da ’ya’ya mata sama da matakin Firamare. (NAN)