Gwamnatin Taliban ta zartar da hukuncin kisa a cikin masallaci
Wannan ne karo na biyu da ake aiwatar da hukuncin
Gwamnatin Taliban ta kasar Afghanistan ta zartar da hukuncin kisa ta hanyar bindigewa a bainar jama’a a cikin masallaci ga wani da aka samu da laifin kisan kai.
Matakin na ranar Talata dai shi ne karo na biyu da ake zartar da irin wannan hukunci tun lokacin da kungiyar ta karbi ragamar mulkin kasar a 2021.
- ’Yan bindiga sun sace manajar banki a Bayelsa
- Gwamnan Kano ya nada ‘dansa’ shugabancin wata hukumar gwamnati
An zartar da hukuncin kisan ne ta hanyar bindigewa a wani gari mai suna Sultan Ghazi Baba da ke lardin Lagman a tsakiyar kasar.
Bayanai sun nuna cewar mahukuntan Taliban ne suka zartar da hukuncin a bainar jama’a domin ya kasance gargadi ga sauran masu aikata laifuffuka.
Kafin zartar da hukuncin a cikin masallaci, sai da aka bayyana sunan mai laifin a matsayin Ajmal dan Naseem, kuma an same shi da laifin kisan mutane biyar ne, saboda haka aka aiwatar da hukuncin a gaban mutane sama da dubu biyu.
Aiwatar da hukuncin kisa a lokacin da kungiyar Taliban ta mulkin Afghanistan tsakanin 1996 zuwa 2001 ya kasance ruwan dare, amma daga lokacin da ta sake dawowa kan madafan iko, wannan ne karo na biyu da hakan ta faru.
To amma duk da cewa ba kasafai sabuwar gwamnatin ke aiwatar da kisa a kan wadanda aka sama da laifi ba, amma sau da dama ana yin bulala ga wadannan suka aikata wasu laifufuka, da suka hada da sata, zina da kuma shan giya.
(RFI)