Gwamnatin Tambuwal za ta samar da makabartu 7 a birnin Sakkwato
Gwamnatin Jihar Sakkwato a karkashin jagorancin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ta yi alkawarin samar da filayen makabartu guda bakwai da zagaye su a rika binne mutane saboda karancin wurin binne mutane su a birnin Sakkwato tun lokacin da manyan makabartu uku na birnin da suke Tudun Wada da Giginyu da Jegawa suka cika.Kwamishinan Filaye da […]
Gwamnatin Jihar Sakkwato a karkashin jagorancin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ta yi alkawarin samar da filayen makabartu guda bakwai da zagaye su a rika binne mutane saboda karancin wurin binne mutane su a birnin Sakkwato tun lokacin da manyan makabartu uku na birnin da suke Tudun Wada da Giginyu da Jegawa suka cika.
Kwamishinan Filaye da Gidaje da Safiyo na Jihar Alhaji Bello Abubakar Guiwa ne ya bayyana haka ga manema labarai a Sakkwato, inda ya ce gwamnatin ta lura mutane suna shiga wahala da damuwa in aka yi musu rasuwa ta yadda sai an dauki mutum zuwa wajen gari da nisa domin a rufe shi, don haka ba za ta bari a ci gaba da wahalar ba, za ta samar da filayen ba da jimawa ba.
Kwamishinan ya kara da cewa sannan shiri ya yi nisa sosai na kara gina gidaje 250 a Unguwar Bado da gwamnatin jihar za ta yi wa ma’aikata kari a ka wadanda tsohuwar gwamnati ta gina a Kalambaina da Gidan Man Ada da aka kusan kammalawa, don saukaka wa ma’aikatan karancin gidaje da suke fama da shi.
Kwamishina Bello Guiwa ya ce gwamnatinsu ta bayar da ayyukkan hanyoyin mota da suka hada da Kantin Sani zuwa Bayan Gari da mayar da titin Sarkin Musulmi Dasuki tagwaye da na Wali Bako da Madam Karo zuwa NNPC duk a cikin Unguwar Mabera da kuma wasu tituna a Runjin Sambo, kuma duk za a yi su ne don kawata gari da fadada shi da inganta hanyoyin motar da ake da su. “Shiri ya kammala na dauke Kasuwar Katako daga inda take zuwa garin Madorawa, su ma kanikawa za mu yi musu dan kauyen kanikawa da zai zama duk wani abu da ake bukata na gyara za a same shi a can,” inji Guiwa.
Da ya juya kan tashoshin mota da ke fadar jihar, ya ce za a sake fasalinsu inda za a gina sababbin tashoshin mota a jihar tare da kashe wasu don gyara da tsabtace garin tare da dawo da fasalinsa na farko.