Gwamnatin Taraba ta soma kwance wa tsohon Mukaddashin Gwamnan Jihar zane a kasuwa

Ga dukkan alamu gwamnatin Jihar Taraba a karkashin Gwamna Darius Ishaku ta soma kwance wa tsohon Mukaddashin Gwamnan Jihar Alhaji Sani Abubakar danladi zane a kasuwa. Haka ya fara fitowa fili ne bayan wani umurni da gwamnatin jihar ta bayar na korar dukkan ma’aikatan da aka dauka aiki a lokaci mulkinsa. Dakatar da wadanda aka […]

Gwamnatin Taraba ta soma kwance wa tsohon Mukaddashin Gwamnan Jihar zane a kasuwa
Gwamnatin Taraba ta soma kwance wa tsohon Mukaddashin Gwamnan Jihar zane a kasuwa

Ga dukkan alamu gwamnatin Jihar Taraba a karkashin Gwamna Darius Ishaku ta soma kwance wa tsohon Mukaddashin Gwamnan Jihar Alhaji Sani Abubakar danladi zane a kasuwa. Haka ya fara fitowa fili ne bayan wani umurni da gwamnatin jihar ta bayar na korar dukkan ma’aikatan da aka dauka aiki a lokaci mulkinsa.

Dakatar da wadanda aka dauka aikin a lokacin mulkin Mukaddashin Gwamnan na kunshe ne a cikin wata takardar sanawar, dauke da sanya hannun Babban Sakatare a ofishin Sakataren Gwamnati Jihar mai suna Malam Ayuba Damphar.
Sanarwa ta ce gwamnati ta dauki matakin ne saboda rashin kudi, kuma sanarwar ta ce wadanda aka dauka aiki jim kadan bayan faduwar tsohon Gwamnan Jihar danbaba Suntai a jirgi a shekarar 2012 an dakatar da su daga aiki.
Masu fashin baki a jihar suna kallon matakin na gwamnatin Darius da cewa yunkurin bincikar tsofaffin mukaddassan Gwamnan Jihar Alhaji Garba Umar da Alhaji Sani Abubakar danladi da a lokutansu ne aka dauki ma’aikatan.
Sun ce ba su ji mamaki ba da gwamnatin Darius ta yi watsi da abubuwan da gwamnatin Garba Umar ta aiwatar ba, illa yadda tun ba a je ko’ina ba aka soma korar wadanda Sani Abubakar ya dauka aiki.
Wani mazaunin Jalingo mai suna Mista Dabid Simon ya ce bai yi mamakin dakatar da ma’aikatan da tsohon Mukaddashin Gwamnan ya dauka aiki ba, domin da ma aikin kudi Sani danladi ya yi wa Janar T.Y. danjuma na tabbatar da ganin Mista Darius Ishaku ya zama Gwamna a jihar.
Shi kuwa Malam Sani Haruna cewa ya yi dakatar da wadanda aka dauka aiki a lokacin Sani Abubakar ya nuna a cewa ba za a dade ba, za a ga Sani Abubakar da Gwamnan Darius a rana.
“Ga dukkun alamu gwamnatin Darius za ta binciki Sani Abubakar kan zargin tsiyata jihar,” inji Sani Haruna. Ya ce tsohon Mukaddashin Gwamnan ya bar asusun gwamnatin jihar ba ko sisin kwabo.
Ya ce, baya ga haka watakila an yi haka ne don korar wasu aiki da nufin a maye gurbinsu da wasu ta hanyar nuna bambancin addini ko kabilanci, musamman da yake ana zargin gwamnatin da bullo da wasu manufofi da suke nuna cewa za a fifita wasu a jihar.
Sai dai a martanin da Kakakin Gwamnan Malam Hassan Mijinyawa ya mayar ya ce an samu korafe-korafe aan yadda aka dauki ma’aikatan ne a lokacin tsohon Mukaddashin Gwamna cewa ba a bi dokokin daukar ma’aikata ba.
Malam Mijinyawa ya ce an dauki ma’aikata tare da yi wa wasu canjin wurin aiki a cikn sirri wanda hakan ya saba wa doka.
Ya ce dakatar da ma’aikatan da aka dauka lokacin Alhaji Garba Umar an yi ne bisa la’akari da hukuncin Kotun koli da ya ce gwamnatin Garba Umar haramtatciya ce saboda haka duk abubuwan da gwamnatinsa ta aiwatar shi ma bai da tasiri.