Gwamnatin Tarayya ba ta da hannu a rikicin Boko Haram- Namadi

Mataimakain Shugaban kasa Namadi Sambo ya wanke gwamnatin tarayya inda ya ce ba ta da hannu a cikin rikicin Boko Haram da ya addabin kasar nan, don haka jita-jitar da ake yadawa cewa da hannunta a ciki ba gaskiya ba ne.Ya bayyana hakan ne a lokacin a fadar Sarkin Kano lokacin da ya jagorancin wakilan […]

Gwamnatin Tarayya ba ta da hannu a rikicin Boko Haram- Namadi
Gwamnatin Tarayya ba ta da hannu a rikicin Boko Haram- Namadi

Mataimakain Shugaban kasa Namadi Sambo ya wanke gwamnatin tarayya inda ya ce ba ta da hannu a cikin rikicin Boko Haram da ya addabin kasar nan, don haka jita-jitar da ake yadawa cewa da hannunta a ciki ba gaskiya ba ne.
Ya bayyana hakan ne a lokacin a fadar Sarkin Kano lokacin da ya jagorancin wakilan gwamnatin tarayya don jajanta wa al’ummar Jihar Kano dangane da harin bam da aka kai Masallacin Juma’a na Kano, inda aka kashe fiye da mutane 100.
 “Ya kamata mu fahimci wannan al’amarin ya fi karfin batun siyasa, inda jama’a suke cewa gwamnati ce take daukar nauyin abin da yake faruwa. Gwamnati ba ta da hannu a ciki. Abin da gwamnati ta dukufa wajen yi shi ne, kare rayuka da dukiyoyin ’yan kasa da kuma samar da zaman lafiya a kasa.
 “Idan aka yi batun tsaro a kasa, to kashin bayan tsaro ya ta’allaka ne a ofishin mai bada shawara na musamman ga shugaban kasa a kan tsaro, wannan ofishin Musulmi daga Jihar Sakkawato wanda yake jikan  Shehu Usman danfodiyo ne yake rike da shi. Na biyu shi ne Ministan tsaro, wato mai ritaya Janar Aliyu Gusau wanda shi ma Musulmi ne daga Jihar Zamfara, sai Sufeto-Janar na ’Yan sanda Suleiman Abba, wanda muke tare da shi a nan, shi ma Musulmi ne daga Jihar Jigawa.
 “Mataimakin Shugaban kasa shi ma Musulmi ne daga Zariya da ke Jihar Kaduna. Babu yadda za a ce dukkanmu Musulmi daga Arewa sannan mu nade hannunmu duk da matsayin da Allah Ya ba mu, sannan mu zura ido mu ci gaba da kallon munanan abubuwan takaici da ke faruwa a yankinmu da kuma Najeriya,” inji Namadi.
Kan yadda za a magance matsalar tsaro sai Sambo ya ce dole sai ’yan kasa sun ba gwamnati da jami’an tsaro hadin kai.
 “Ina so in yi amfani da wannan dama don in bukaci wani abu daga gare ka, Ranka ya dade, ina so ka yi wa mutane umarni bada hadin. Hanya daya mai bullewa ke nan don a kawo karshen matsalar tsaro a kasar nan,” Inji shi.
Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Muhammad Sanusi na II, ya bukaci gwamnatin tarayya ta gudanar da binciken kwakwaf don mangance faruwar irin haka a gaba.
 “Mun yi imani babu abin da zai faru gare mu face abin da Allah ya kaddara, ba yadda za a magance masifa ta hanyar amfani da fushi da kuma sakaci, za ka magance fushi ta hanyar hakuri da juriya, amma muna bukatar a gudanar da kwakkwaran bincike.” Inji mai martaba.