Gwamnatin Tarayya ce ke rike da Zakzaky ba wani ba – Yakubu Yahaya

Ci gaba da tsare Shugaban Kungiyar IMN ta mabiya Shi’a, Sheikh Ibrahim Zakzaky na ci gaba da jawo cece-ku-ce a tsakanin Gwamnatin Tarayya wadda ta ce babu hannunta a ciki, Gwamnatin Jihar Kaduna ce ke tsare da shi. Aminiya ta tuntubi Sheikh Yakubu Yahaya Katsina, jagoran mabiya Shi’ar domin jin dalilinsu kan wannan tsarewa da […]

Gwamnatin Tarayya ce ke rike da Zakzaky ba wani ba – Yakubu Yahaya

Malam Yakubu Yahaya Katsina

Ci gaba da tsare Shugaban Kungiyar IMN ta mabiya Shi’a, Sheikh Ibrahim Zakzaky na ci gaba da jawo cece-ku-ce a tsakanin Gwamnatin Tarayya wadda ta ce babu hannunta a ciki, Gwamnatin Jihar Kaduna ce ke tsare da shi. Aminiya ta tuntubi Sheikh Yakubu Yahaya Katsina, jagoran mabiya Shi’ar domin jin dalilinsu kan wannan tsarewa da kuma masu alhakin tsarewar:

Gwamnatin Tarayya ta ce ba ita ke rike da Sheikh Zakzaky ba, amma ku kun ce ita ce, mene ne dalilinku?

In za mu iya tunawa Yarima Salman Abdul’aziz a wata hira da ya yi da jaridar Times ta Amurka ya ce su suka umarci Gwamnatin Najeriya ta kawo karshen Malam Zakzaky da kungiyarsa ta Shi’a saboda su rage tasirin Iran a Afirka, kuma zuwa yanzu sun samu nasara kusan kashi 90 cikin 100 . Wannan shi ne abu na farko da za mu fahimta. Kwanan nan kuma Farfesa Ibrahim Ahmed Makari wanda limamin Masallacin Abuja ne ya je Ghana wajen Mauludi ya gabatar da makala inda ya ce akwai wani shugaban wata cibiyar Musulmi da ke Saudiyya wadda cibiya ce ta tattara malamai na duniya masu da’awa da wa’azi. To mataimakin shugaban ya zo nan Najeriya wanda bai fadi rana ko shekara ba, amma ga alama kafin abin da ya faru a Zariya ne ya zo. Ya ce mutumin ya zo inda aka tara su kamar su 10 amma shi bai san matsayinsa ba. Sai ya ce to abin da ya kawo su nan shi ne yaya za a yi a yi fada da Shi’a da Sufaye. Shi kuma Farfesa sai ya ce masa mu nan kasar ba abin da ya dame mu ke nan ba, abin da ya dame mu shi ne batun rashin addini da wadansu ba su da shi ga kuma karancin makarantu da masallatai da sauran abubuwa na ci gaba. To ka ga abubuwa biyu ke nan.

An rushe gida da makaranta da kuma kashe mabiya bayan Shehin Malamin tare da kashe masa yara uku da harbin shi kansa Zakzaky gami da kama shi tare da matarsa an kulle su yau shekara 4 ke nan. An je kotu inda ta bayar da umarnin sakin Malam tare da biyansa diyya amma hakan bai samu ba saboda an ki bin umarnin kotun. Shin wane ne ke da kasar nan? Wane ne doka ta san cewa shi ke jagorantar kasar nan? Wane ne Babban Kwamandan gudanar da dukkan al’amurran kasar nan? Za mu ga cewa kasar tana da doka da oda, Shugaba da kuma bangarori daban-dabam na tsaro, kuma shi Shugaban Kasa shi ne Babban Kwamanda wanda duk umarni a hannunsa yake. Doka ta dora masa yin kariya ga kowane irin al’amari na kasar nan wanda ya hada har da rayuka da dukiyar al’ummar kasar nan. Kazalika, babu mai ikon harba harsashi daya ba tare da izinin Shugaban Kasa ba, domin shi ne mai bayar da izini. Za ka sha mamaki a ce Shugaban Kasa yana Kaduna amma ana barin wuta a Zariya kwana biyu yini uku a ce wai Shugaban Kasa bai sani ba.

Sojojin da suka yi wannan aiki ba karkashin Gwamna suke ba, suna karkashin Shugaban Kasa ne. Akwai ma wani taron da aka yi kwanan nan a nan Kaduna, ga shi (Gwamna) El- Rufa’i ga Shugaban Kasa inda shi Gwamna yake gode wa sojoji a kan magance masu matsalar masu satar shanu da masu garkuwa da mutane, sannan sun magance masu matsalar ’yan Zakzaky. Nan aka tafa, duk wanda ke wurin babu wanda bai yi tafi ba sai mace daya kawai.

Ke nan kana ganin SheikH Zakzaky yana wajen Gwamnatin Tarayya ce?

Maganar a ce hannun wa Sheikh Zakzaky yake, magana ce da ake son wawantar da jama’a. Hatta kotun da aka je ai ta Gwamnatin Tarayya ce. Shi kansa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ai ya je ziyara a tsakanin Katar ko Dubai kuma an yi masa magana a kan batun Malam inda ya ce su ba za su yarda da gwamnati a cikin wata gwamnati ba. Saboda Iran tana goyon bayan Zakzaky domin a kafa daular Musulunci wadda su kuma ba su yarda da wannan ba. Babu wata ja-in-ja Sheikh Zakzaky a hannun Gwamnatin Tarayya yake.

To me ya sa ake yawan zarginku cewa kuna kokarin kafa wata gwamnati ce a Najeriya?

Ta yaya wanda ba ya da ko yashi na sayarwa a hannunsa da zai samu kudi a ce zai kafa gwamnati ko yake da gwamnati? Mabiya Shi’ar da ke nan Najeriya an sanya mu a tsakiya kawai saboda wata bukata ta siyasa a tsakanin Saudiyya da Iran bisa dalilan cewa Saudiyya na son tauye tasirin da kasar Iran ke yi ta fuskar fahimtar addini a Arewancin Najeriya, yayin da ita ma Saudiyya ke son nuna irin nata karfin a kan ita Iran. Saboda haka, sai ake amfani da mu’amalar da ke tsakanin ’yan Shi’ar da kasar Iran wadda kuma ba su taka doka ba a kan haka kamar yadda Kiristoci suke da mu’amala da Batikan, kamar yadda ’yan Izala suke da ita Saudiyya ko ’yan dimokuradiyya masu yi da Amurka, wadansu ’yan Tijjaniya ma suna yi da Moroko da sauran irinsu, haka muma muke yi. Wato dai giwaye ne biyu suke fada wanda mu ciyawar muke shan wuya maimakon su tsaya can su yi abinsu bisa fako.

Ga shi an mayar da Sheikh Zakzaky gidan yari me za ka ce?

Wannan ma wata hikima da Amurka ta sa aka yi, domin tana son gwamnati ta fito da Sowore wanda har Dasuki ya ci arzikinsa. Sun lura cewa, in aka ce a sako duk wadanda ke hannun jami’an tsaron nan kamar yadda kotu ta umarta, to lallai har shi Malam Ibrahim za a sako, saboda haka, sai suka yi sauri suka kai shi gidan yari da sunan dan ta’adda.

Me malam zai ce game da walwalar da Zakzaky ya samu a yanzu na zaman gidan yari sabanin wuri karami, sannan wane mataki kuke shirin dauka nan gaba kan batun sako shi?

Bambancin kawai shi ne fadin fili, amma duk kuncin iri daya ne. Iyaka a ce wannan za ka fito daga cikin daki ka yi yawo tsakar gida kuma ga jama’a amma kuma ba ka da ’yanci domin za a mayar da kai a rufe. Sannan batun daukar wani mataki, muna nan muna kokarin sake zuwa kotu domin a sakar mana malaminmu, ya je ya nemi magani tunda gwamnati ba ta iyawa, in ya so sai a ci gaba da shari’a har gaskiya ta yi halinta.

Wane kira za ka yi ga mutane?

Ina kira ga magoya bayanmu su ci gaba da hakuri tare da addu’a kamar yadda aka saba. Jama’a kuma su kara sa ido da kunnuwa su ji ko su gani ina ne muka yi duk wasu kalaman batanci da ake yi a kan cewa, muna zagin sahabbai.