‘Gwamnatin Tarayya na iya kasa biyan albashin watan Oktoba’
Gwamnatin Tarayya ta ce tana iya kasa biyan albashin wattan Oktoba idan Majalisar Dokoki ta kasa ta ki yin gyara kan kasafin kudin bana.Ministar Kudi Misis Ngozi Okonjo-Iweala ce ta bayyana haka a ranar Litinin da ta gabata lokacin da take tattaunawa da wani shirin harkokin siyasa na gidan Rediyon RayPower da aka kama a […]

Gwamnatin Tarayya ta ce tana iya kasa biyan albashin wattan Oktoba idan Majalisar Dokoki ta kasa ta ki yin gyara kan kasafin kudin bana.
Ministar Kudi Misis Ngozi Okonjo-Iweala ce ta bayyana haka a ranar Litinin da ta gabata lokacin da take tattaunawa da wani shirin harkokin siyasa na gidan Rediyon RayPower da aka kama a Abuja.
Ministar ta ce, “An kai wani matsayi da dole a yi gyara, kuma wannan ne ya sa Shugaban kasa ya aika da bukatar gyaran ga Majalisar Dokoki ta Tarayyya. Ina jin za mu ci gaba ne na wani lokaci, kuma a wani lokacin akwai bukatar a sanya hannu kan gyaran, saboda nan da Satumba ko Oktoba, muna iya gaza biyan albashi. Muna tattaunawa da kwamitoci da shugabannin majalisar ta hanyar da ta dace domin magance wannan matsalar. Amma wani misali shi ne muhimmi shi ne albashi, kuma tsakanin nan da Okoba za mu bukaci Naira biliyan 32.”
Da aka ambaye ta kan halin da tattalin arzikin kasar nan ke ciki, Minisar Kudin ta hanzarta watsi da wani labari da ake yadawa cewa kasar nan ta tsiyace, inda ta ce, tattalin arzikin Najeriya yana da karfi, sai dai ana fama da rashin tsabar kudi ne a ’yan kwanakin nan.
Ta ce, “Muna yin komai a fili game da shi. a koyaushe ina da imanin fada wa ’yan Najeriya halin da ake ciki game da kasafin, bisa lura da tattalin arzkin. Tattalin arzikin Najeriya yana da cikakken karfi, amma a cikin karfin tattalin arziki kana iya fuskantar rashin tsabar kudi. kasashen waje suna kallon mu a matsayin masu karfin tattalin arziki. Don haka yanzu matsalar da muke ciki na wani karamin lokaci ne.”
Idan za a iya tunawa Shugaba Goodluck Jonathan ya sake maida wa majalisar kasafin ne domin gudanar da sauye-sauye inda aka samu rahoton cewa ya rage kasafin da Naira biliyan 56 daga kasafin da Majalisar Wakilai ta ki amincewa da shi a makon jiya.