Gwamnatin Tarayya na shirin sake fasalin tsarin JSS da SSS a makarantun sakandare

Tsarin raba ƙaramar sakandare (JSS) da babbar sakandare (SSS), bai cimma manufar da aka ƙirƙire shi dominta ba.

Gwamnatin Tarayya na shirin sake fasalin tsarin JSS da SSS a makarantun sakandare

Ministan Ilimi, Tunji Alausa

Gwamnatin Tarayya ta ba da umarnin sake fasalin tsarin ilimin sakandire a Najeriya, bayan ta ce bincike ya nuna cewa sama da yara miliyan 20 da suka fara karatun firamare ba sa kai wa matakin babbar makarantar sakandare.

Ministan Ilimi, Maruf Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin ƙaddamar da Kwamitin Aiwatarwa da Saka Ido na Ma’aikatar Ilimi a Abuja.

Ya ce tsarin da ake bi a yanzu, wanda ya raba makarantar sakandare zuwa ƙaramar sakandare (JSS) da babbar sakandare (SSS), bai cimma manufar da aka ƙirƙire shi dominta ba.

A cewarsa, tsarin na ɗaya daga cikin abubuwan da ke haifar da katsewar karatun yara da dama bayan sun kammala matakin ƙaramar sakandare.