Gwamnatin Tarayya ta ayyana hutun Ranar Samun ‘Yanci Kai a Nijeriya
Gwamnatin tana yaba wa hakuri da jajircewar ’yan Nijeriya maza da mata.
Gwamnatin Tarayya ta ayyana Talata, 1 ga watan Oktoba a matsayin ranar hutu albarkacin cikar Nijeriya shekara 64 da samun ’yancin kai.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da Babbar Sakatariyar Ma’aikatar, Dokta Magdalene Ajani, ta fitar a ranar Asabar.
- Isra’ila ta hallaka jagoran Hezbollah Hassan Nasrallah
- An sanar da Vinicius cewa zai lashe kyautar Ballon d’Or
Ya sake nanata bukatar ‘yan Nijeriya da su yi tuntuntuni a kan “aikin da jarumai ’yan mazan jiya suka yi a baya da kuma kwarin gwiwa kan ayyukan da ke gaba”, yana mai cewa “kyakkyawar makoma a Nijeriya za ta tabbata ne kadai idan muka hada kai.”
Ministan ya ce duk da cewa tarin kalubalen da suke fuskantar Nijeriya ba iya kasar suke shafa ba, amma gwamnati na iya bakin kokarinta wajen ganin ta magance su.
Ministan ya kuma taya dukkan ’yan kasar na gida da na ketare murnar zagayowar ranar a yayin da yake yaba wa hakuri da jajircewar ’yan Nijeriya maza da mata, inda ya bayyana cewa sadaukarwar da suka yi ba za ta zama a banza ba.