Gwamnatin Tarayya ta ba masu burodin rogo bashin biliyan 2
Gwamnatin Tarayya tare da hadin gwiwar Bankin Masana’antu ta bayyana ta ba masu burodin rogo bashin Naira 2.2 don su bunkasa harkarsu.Mutane 174 wadanda mambobin kungiyar masu yin burodi na Najeriya ne suka amfana da bashin gwamnatin tarayya.Ma’aikatar Noma da Bunkasa Karkara ta Tarayya ne ta jagoranci raba bashin.Manajin-Daraktan Bankin Masana’antu, Mista Rasheed Olaoluwa ya […]
Gwamnatin Tarayya tare da hadin gwiwar Bankin Masana’antu ta bayyana ta ba masu burodin rogo bashin Naira 2.2 don su bunkasa harkarsu.
Mutane 174 wadanda mambobin kungiyar masu yin burodi na Najeriya ne suka amfana da bashin gwamnatin tarayya.
Ma’aikatar Noma da Bunkasa Karkara ta Tarayya ne ta jagoranci raba bashin.
Manajin-Daraktan Bankin Masana’antu, Mista Rasheed Olaoluwa ya ce wadanda aka ba bashin za su yi amfani da shi wajen sayan injin gasa burodi na zamani da sauran kayayyakin yin burodi na zamani don samar da burodi mai inganci da tsabta a kasa, an kuma raba bashin ne don a samar da kashi 20 cikin 100 na garin rogon da za a hada cikin alkamar da za a yi burodin rogo da ita.
Ya ce dalilan hakan ne ya sa aka ware Naira biliyan 2.2 don a cimma wannan burin.
“An raba wadanda za su amfana da wannan tsarin kashi biyu. An riga an raba Naira miliyan 989 ga mutane 100. Ga sauran mutane 74 kuma; 60 daga cikinsu ne suka cika dukkan ka’idojin karbar bashin da ake bukata, inda nan gaba za a ba su kashi 50 cikin 100 na kudin wanda ya kama Naira miliyan 537.93.
A karshe ya bukaci wadanda aka ba bashin su tabbata sun yi amfani da shi yadda ya dace.