Gwamnatin Tarayya ta bai wa kowace jiha tirelar shinkafa 20
Ministan ya ce wannan wani mataki ne na daƙile ƙarancin abinci a ƙasar nan.
Gwamnatin Tarayya ta raba wa kowace jiha a Najeriya ciki har da Babban Birnin Tarayya, Abuja tirelar shinkafa 20 domin rage raɗaɗin ƙaracin abinci.
Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris ne, ya bayyana hakan bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya (FEC), na ranar Litinin.
- UAE ta dawo bai wa ’yan Najeriya biza — Gwamnatin Tarayya
- Kotu ta tabbatar da nadin Sanusi II a matsayin Sarkin Kano
Ministan, ya ce wannan shi ne mataki na farko da gwamnati ta ɗauka na magance matsalar ƙarancin abinci a ƙasar nan.
Ya kuma yi kira ga gwamnonin da su tabbatar an raba kayan ga marasa galihu a jihohinsu.
Wannan dai na zuwa ne bayan da Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS), ta fitar da wani rahoto da ya nuna hauhawar farashi ya ƙaru zuwa kashi 34.19 a watan Yuni.
NBS ta ce idan aka kwatanta da watanni baya, kayayyaki sun sake yin tashin gwauron zabi a Najeriya.
A gefe guda kuma ’yan Najeriya na ci gaba da kokawa kan halin matsi da ake fama da shi, yayin da kuma matasa a ƙasar ke shirin tsunduma zanga-zanga a farkon wagan Agusta.
Sai dai batun shiga zanga-zangar ya haifar da cece-kuce da tada jijiyar wuyar tsakanin matasa da malamai a ƙasar.